logo

HAUSA

Don tinkarar hauhawar farashi ake neman shiga tsarin BRICS

2023-07-25 18:58:43 CMG Hausa

A kwanakin nan, hauhawar farashin kayayyaki a tarayyar Najeriya ta yi tsanani, har ma rahotanni na cewa, karuwar farashin kayayyakin abinci ta kai kashi 25%. Ko yaya yanayin farashi a wuraren ku yake? Da fatan babu matsala.

Hakika farashin kayayyaki yana nuna yadda yanayin tattalin arzikin wata kasa yake ciki, kana yana da alaka da yanayin tattalin arziki, da harkokin siyasa na kasa da kasa. Misali, yadda baitulmalin kasar Amurka ke kara ruwan kudin ajiya da na bashi a kai a kai, ya sa darajar kudin kasar wato dalar Amurka, wadda ake yawan yin amfani da ita wajen cinikin kasa da kasa karuwa, lamarin da ya haddasa raguwar darajar kudin sauran kasashe, da tashin gwauron zabin farashin kayayyaki a kasuwanninsu, da karuwar bashin da ake binsu irin na dalar Amurka.

Ban da haka, rikicin da ake yi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, da dimbin takunkumin da kasashen yamma ke sakawa sakamakon rikicin, sun haddasa matsalar hauhawar farashin makamashi da hatsi, wadda ita ma ta tsaurara yanayin da kasashe masu tasowa ke ciki na fama da hauhawar farashin kaya.

A lokacin da kasashen yamma suka yi biris da moriyar kasashe masu tasowa, ko kuma aka dauki matakan da ka iya lahanta moriyarsu, to tilas ne su kasashe masu tasowa su juya ga tsarin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa, don tabbatar da samun isashen goyon baya. Wannan shi ne dalilin da ya sa tsarin BRICS ke janyo hankalin dimbin kasashe masu tasowa. A cewar Anil Sooklal, babban jami’in kasar Afirka ta Kudu mai kula da harkoki masu alaka da tsarin BRICS, wasu kasashe fiye da 40, sun riga sun bayyana niyyarsu ta neman izinin shiga tsarin BRICS, ciki har da dukkan manyan kasashe masu tasowa na duniya.

Wani taro mai alaka da aikin tsaro da ake gudanarwa karkashin laimar tsarin BRICS a kasar Afirka ta Kudu, shi ma ya nuna yadda tsarin ke jan hankalin kasashe daban daban, inda ban da membobin kungiyar 5, wato kasashe Brazil, da Rasha, da Indiya da Sin, da kuma Afirka ta Kudu, sauran kasashen da suka hada da Belarus, da Iran, da Saudiyya, da Masar, da Burundi, da hadaddiyar daular Larabawa ta UAE, da Khazakstan, da Cuba, da dai sauransu, su ma sun tura wakilai don halartar taron.

Kana a cewar kasar Afirka ta Kudu, wadda za ta karbi bakuncin taron koli na BRICS da zai gudana a wata mai zuwa, a taron dake tafe ma za a dora muhimmanci kan tattauna batun habaka tsarin BRICS, inda za a kara yawan mambobinsa.

Hakika kasashe masu tasowa, sun darajanta kokarin da kasashen BRICS suke yi, na maye gurbin dalar Amurka da sauran kudi. Tun daga shekarar 2010, kasashen BRICS sun kaddamar da tsarin hadin gwiwa tsakananin bankunansu, don ba da izinin yin amfani da kudi na kansu wajen gudanar da cinikin kasa da kasa. Kana tsarin BRICS ya bukaci mambobinsa da su kara yin hadin gwiwa ta fuskar kudi da ya shafi musaya, da zuba jari ta kudin kasashen, da dai sauransu, don neman kafa wani tsarin kudi na kasa da kasa da ya kunshi mabambantan kudi na kasashe daban daban. Wannan manufa ta zama tudun-mun-tsira ga dimbin kasashe masu tasowa, wadanda suke fuskantar matsin lamba a fannin tattalin arziki.

Ban da haka, girman kasashen BRICS, da karfin tattalin arzikinsu, su ma sun tabbatar da yiwuwar samun ci gaban tattalin arziki, ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Yanzu haka yawan al’ummun kasashen BRICS ya kai kashi 42% cikin jimillar al’ummun daukacin duniya. Kana yawan GDPn kasashen BRICS ya riga ya haura na kungiyar G7, wadda ke kunshe da manyan kasashe masu sukuni guda 7. Haka zalika, bankin neman ci gaba na BRICS, shi ma zai taka rawar samar da kudin musaya bisa bukatar da ake samu cikin gaggawa, don tabbatar da tsaron mambobin kasashe a fannin hada-hadar kudi.

A karshe dai, ana sa ran ganin tsarin BRICS ya zama wani muhimmin dandalin da daukacin kasashe masu tasowa ke iya gudanar da hadin gwiwa a ciki, bisa yadda kasashen Afirka, da sauran kasashe masu tasowa na sauran yankuna ke kokarin neman shiga cikin tsarin.

Ta la’akari da yanayin karuwar kason da kasashen BRICS ke samu cikin tattalin arzikin duniya, hadin gwiwarsu za ta taka muhimmiyar rawa, a fannin kula da harkokin kasa da kasa, da samar da gudummawa ga yunkurin kare zaman lafiya, da raya tattalin arzikin duniya, gami da kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Bello Wang)