logo

HAUSA

Kan Mage Ya Waye, Turawan Yamma A Sake Lale Kan Yamadidin “Tarkon Bashin Sin”

2023-07-22 16:50:15 CMG Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza 

Ya dace zuwa yanzu kowa ya fahimci kulafacin da Turawan Yamma ke nunawa a kan kawancen da kasar Sin ke yi da kasashen duniya musamman masu tasowa wajen samar da damammaki domin cin gajiyar juna.

Shaci-fadi da farfagandar wofi sun mamaye rahotannin da kafafen yada labarun yamma ke bayarwa a duk wani abu da ya shafi kawancen ci gaba na Sin da kawayenta.

Ko da Turawan suka ga sun kasa tarwatsa kawancen, sai suka bullo ta bayan gida ta hanyar yamadidin cewa kasar Sin na dankara wa kasashe masu tasowa basussuka na rashin imani inda suka yi wa abin lakabi da “Tarkon Bashin Sin”.

Amma domin rabe zare da abawa, wani bincike da aka gudanar kwanan nan a wasu kasashe kamar Pakistan, Kenya, Zambia da Sri Lanka, ya yi tonon silili ga yamadidin kambama basussukan da Sin ke bai wa kasashen domin ayyukan bunkasa ababen more rayuwa da raya kasa.

Kididdiga ta nuna cewa, daga cikin bashin da Kenya ta ci a kasashen waje kimanin Dala biliyan 36.66 zuwa watan Maris din 2023, kashi 17.2 cikin dari ne na Sin, a yayin da hukumomin kudi na tsakanin bangarori da dama ke bin ta kaso 46.3%, ciki har da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da bankin duniya da sauransu. Ita kuwa Pakistan zuwa watan Afrilun 2023, tana da bashin waje a kanta Dala biliyan 125.702, daga ciki du-du-du na Sin bai wuce Dala biliyan 20.375 ba, kimanin kashi 16.2 cikin dari.

A Zambia, basussukan waje da kasar ta ci zuwa karshen 2022 sun kai na Dala biliyan 18.6, daga ciki Dala biliyan 6 ne na Sin. Haka nan idan aka dubi Sri Lanka, basussukanta na waje zuwa watan Maris, 2023 sun kai Dala biliyan 27.6, daga wannan adadin kwata-kwata na Sin bai wuce Dala biliyan 3 ba, kimanin kashi 10.8 a cikin dari.

Don haka ta ina ne basussukan Sin suka zama karfen kafa ga kasashen da take kawance da su? Ko dai abin nan ne da Hausawa ke cewa, “idan an tsani mutum ko ruwa ya shiga sai a ce ya tayar da kura.”

An ce “gwano ba ya jin warin jikinsa”, su kasashen yamma sun fi kowa dankara wa kasashe bashi da mugun kudin ruwa. Ba zan manta ba, shi ya sa a zamanin mulkin tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo (1999-2007) ya niki gari har kasashen Turawan na yamma ya shaida musu cewa Nijeriya ba za ta iya biyan basussukan da suke bi ba, saboda dankaren kudin ruwa, sai dai su yafe kawai!

Kamar yadda Obasanjo ya koka da dankaren kudin ruwan basussukan yamma, shi ma shugaban wata cibiyar binicke kan bunkasa tattalin arziki da ci gaba a zamanance ta Asiya da ke Pakistan, Shakeel Ahmad Ramay ya ce, “Babbar matsalarmu ita ce basussukan da muka ci daga hukumomin kudi na kasashen yamma, Pakistan ba za ta iya biyan su ba saboda basussuka ne masu dankaren kudin ruwa.”

Bayanai daga Bankin Duniya sun tabbatar da cewa kashi uku bisa hudun basussukan da Afirka ke ka-ka-ni-ka-yi da su daga cibiyoyin kudi ne na kasashen duniya amma ba kasar Sin ba.

Shi ya sa mataimakin sakataren kungiyar kawancen Sin da Zambia, Chibeza Mfun ya ce, “idan ma akwai abin da ya fi ci mana tuwo a kwarya a matsayinmu na kasa, shi ne biyu bisa ukun basussukan da ake bin mu. Ba kasar Sin ke bin mu biyu bisa uku ba, masu kawo gudunmawa ne daga kasashen yamma da cibiyoyin kudi.”

Maimakon yamadidi, kamata ya yi Amurka da sauran kasashen yamma su dubi yadda suke bautar da kasashe masu tasowa da kudin ruwan da suke lafta wa basussukan da suke bin su, da yayyafa wa rikicin Ukraine da suka kunna ruwa wanda yake barazana tare da nakasa kasashe masu tasowa. A halin yanzu dai kan mage ya waye, batun yamadidin “Tarkon Bashin Sin”, gidan toka ne da ake son ginawa a tsakiyar teku!