logo

HAUSA

Wane Irin Hadari Amurka Take Son Ta Kawar?

2023-07-22 15:27:22 CMG HAUSA

DAGA MINA

 Kwanan baya, wasu ’yan siyasa sun bayyana a dandalolin kasa da kasa cewa, ba su neman katse hulda da Sin, suna son kawar da hadari. To, wane irin hadari Amurka take son ta kawar?

Mujallar “Harkokin Diplomasiyya” ta kasar Amurka ta bayyana cewa, Amurka tana yunkurin kawar da wasu abubuwa da ta kira wai hadari, amma a hakika dai tana son kayyade karfin kasar Sin ne a fannonin dake da nasaba da tsaron kasa, da dakile matsayin Sin a fanonnin muhimman abubuwa da ake amfani da su wajen samar da kayayyaki, da ma rage karfin kasuwannin Sin a duniya. Wannan ba shakka tunani ne na yakin cacar baka! Bunkasuwar Sin ta kawowa fadin duniya damammaki da dabaru da fasahohi na a zo a gani. Idan kuma wadannan su ne hadari, ko shakka babu, hadari ne ga moriyar ’yan siyasar Amurka kawai.

Sai dai a daf da karshen rayuwar George Kennan, wanda ya kirkiro manufofin yankewa tsohon tarayyar Soviet hukunci da sanya mata shingaye don hana bunkasuwarta, ya yi watsi da tunanin na yin yakin cacar baka, abin da ya bayyana cewa, wasu ’yan siyasar Amurka suna ganin cewa, bai kamata Amurka ta bi hanyar da ba ta dace ba, wato yin babakere da hana bunkasuwar sauran kasashe. Fata a nan shi ne, ’yan siyasar Amurka na yanzu su yi koyi da George Kennan, su fahimci kuskurensu, sun dakatar da babakere tare da yin watsi da tunanin cacar baka, sabo da shi ne hadarin da ya kamata ta kawar da shi. (Mai zana da rubuta: MINA)