Sin za ta kara ba da gudummawa ga ci gaban wasanni ta shirya gasar jami’o’in kasa da kasa
2023-07-22 19:37:48 CMG HAUSA
A baya kasar Sin ta sha jagorantar gasar wasanni ta kasa da kasa daban daban, ciki har da gasannin Olympics ta lokacin zafi da ta hunturu. A yanzu kuma, kasar na shirin karbar bakuncin gasar wasannin jami’o’in duniya karo na 31, wadda za ta gudana a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar ta Sin.
Game da hakan, shugaban hukumar shirya wasannin motsa jiki na jami’o’in kasar Turkiyya Mehmet Gunay, ya ce gasar ta Chengdu za ta kara samar da gudummawa ga habakar wasanni. Ya ce "Mun ga yadda kasar Sin ke samun manyan nasarori a baya bayan nan a fannin raya wasanni. A yanzu musamman ta kafafen sada zumunta na yanar gizo, muna samun bayanai a kai a kai game da gasar dake tafe. Muna bibiya sosai, mun kuma gamsu da yanayin shirin da ake yi domin nasarar gasar. Ina jinjinawa kasar Sin bisa cikakken nazari da take yi a fannonin shirya gasanni, da kimiyya da fasahohin wasanni. Muna nazarin wadannan ayyuka na bincike daga nan Turkiyya. Yana da kyau mu yi hadin gwiwa da Sin, musamman domin cin gajiyar darussa, da karfin gwiwa daga nasarorin da ta cimma."
Game da shirin shiga wannan gasa ta birnin Chengdu, Gunay ya ce "Tabbas, mun ware wasannin da muke baiwa fifiko domin cimma nasara. Turkiyya na da kyakkyawan fata na cimma nasara a wasannin taekwondo, da wasan takobi, da harbin kibiya da na tsalle tsalle. Wasanni sun wuce batun gasa kawai, domin kuwa suna share fagen cudanya tsakanin kasashe da al’adu daban daban. Kamar dai nasarorin da Sin ta cimma a baya wajen hade sassan al’adu, musamman yayin gasar Olympic ta birnin Beijing ta wasannin hunturu da aka gudanar a bara.
Gunay ya ce "Abu ne mai muhimmanci gare mu, mu fahimci al’adun kasar Sin, mu kuma kalli abubuwan tarihi da al’adu masu daraja dake kasar, da kuma damar mayar da wasanni wata kofa ta cudanyar al’umma zuwa cudanyar al’adu."
Bugu da kari, mista Gunay ya jinjinawa kwazon kasar Sin na baiwa halittu daban daban kariya, da bunkasa manufofin kare tsirrai, da na kawar da fitar da iskar carbon mai dumama yanayi, da ma yayata wadannan manufa domin wayar da kan al’umma.
Ya ce "Domin gabatar da wannan sako ga sauran al’ummun duniya, yana da kyau a yi amfani da karfin cudanyar sassa daban daban da wasanni ke bayarwa".
An dai tsara gudanar da gasar wasannin jami’o’i karo 31 a birnin Chengdu na lardin Sichuan, tsakanin ranaikun 28 ga watan nan na Yuli zuwa 8 ga watan Agusta, za kuma a gudanar da nau’o’in wasanni 18 yayin gasar.
Arsenal ta sanya hannu kan kwangilar sayen Declan Rice daga West Ham
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta sanya hannu kan kwangilar sayo dan wasan tsakiya Declan Rice daga kungiyar West Ham, kan kudi har fam miliyan 105, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 137.5.
Kocin kungiyar ta Arsenal Mikel Arteta, ya ce dan wasan mai shekaru 24, wanda kuma ya bugawa kungiyar kasar Ingila wasanni 43, yana da kwarewa matuka, ya kuma taka rawar gani a gasar firimiya, da wasannin da kungiyar kasar ingila ta buga a kakar wasanni daban daban. Kaza lika Rice ya taimaka wa kungiyarsa wajen cimma manyan nasarori, tare da nuna hazaka dake tabbatar da dorewarsa a matsayin tauraron dan wasan kwallon kafa.
Yanzu haka dai Rice ya riga ya dora sakon ban kwana da kungiyar West Ham, a shafin sa na yanar gizo, bayan da ya taimakawa kungiyar wajen lashe gasar “Conference League” da ta gabata.
Cikin sakon na sa, Rice ya ce "Ina mamakin ganin karewar zamana na shekaru 10 a nan. West Ham bangare ce ta rayuwa ta, a fannin taka leda da ma rayuwar yau da kullum. Ban kwana da ita ba abu ne mai sauki ba. Ba zan manta da wasu lokuta na musamman a wannan kungiya ba, musamman daren da muka lashe gasar “Conference League” a filin wasa na Fortuna dake Prague-Vršovice, na kasar Czech. Na kuma samu daukaka mai yawa, a matsayin dan wasa da kuma kyaftin din wannan kungiya. Tun daga lokacin da na fara kasance kyaftin din wannan kungiya, nake farin ciki da alfahari da karsashin wasa. Har zuwa yanzu, babban abun da ya faranta min rai ba kamar lashe kofin turai. Kaza lika alaka ta da magoya bayan kungiyar mu babban abun farin ciki ne gare ni da iyalai na. Kun rike mu tamkar ‘yan uwan ku tun ranar da na iso nan. Ina godiya gare ku".