Amurka Na Bukatar Hazakar Kissinger A Harkokin Diplomasiyya
2023-07-21 11:30:58 CMG Hausa
Jiya Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Henry Kissinger a birnin Beijing, hedkwatar kasar, inda ya kira Kissinger mai shekaru 100 da haihuwa tsohon aboki, tare da yaba wa gagarumar gudummowarsa a fannonin kara azama kan ci gaban hulda a tsakanin Sin da Amurka, da kyautata zumuncin da ke tsakanin al’ummomin kasashen 2.
Yau shekaru 52 da suka wuce, Kissinger ya kasance mai ba da taimako ga shugaba Richard Nixon na Amurka na wancan lokaci ta fuskar tsaron kasa, da kuma manzon musamman, ya gana da tsoffin shugabannin kasar Sin, matakin da ya kaddamar da aikin maido da hulda tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.
Ya zuwa yanzu, Kissinger ya ziyarci kasar Sin fiye da sau 100. Tsohon mai shekaru 100 da haihuwa, yana himmantuwa wajen kyautata tuntubar juna tsakanin Sin da Amurka.
Cikin ‘yan siyasar Amurka, Kissinger ya wakilci rukunin wadanda suke nacewa kan tattaunawa da kasar Sin, da kuma daidaita sabani yadda ya kamata. Wadannan ‘yan siyasan sun tsara manufofi masu dacewa game da kasar Sin bisa sanin ya kamata, a kokarin kiyaye muradun Amurka.
A duk lokacin da yake zantawa da shugaba Joe Biden na Amurka ta wayar tarho, ko kuma fuska da fuska, ko lokacin ganawarsa da mista Kissinger a jiya, shugaba Xi Jinping ya sha nanata cewa, dole ne a bi ka’idoji 3 wajen raya hulda a tsakanin Sin da Amurka ba tare da wata matsala ba, wato mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa domin samun nasara tare. Su ne kuma darussan da aka koya daga yadda Sin da Amurka suka yi mu’amala da juna a baya, kana kuma, ka’idoji ne da kasashen 2 za su bi a sabon zamani, yayin da suke mu’amala da juna.
Yanzu haka kusoshin Amurka suna bukatar yin bitar abubuwan da suka faru a tarihi, kuma su kara sanin yadda suke kallon kasar Sin yadda ya kamata, da yadda za su yi mu’amala da kasar Sin, a kokarin biyan bukatunta. Idan sun san amsar hakan, fannonin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Sin za su fadada, ba wai ta fuskar daidaita rikici kadai ba. Ko shakka babu, Amurka na bukatar hazakar Kissinger wajen raya hulda a tsakanin Sin da Amurka. (Tasallah Yuan)