Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Amsa Sunanta
2023-07-19 16:54:00 CMG HAUSA
DAGA Ibrahim Yaya
A bana ne shawarar “ziri daya da hanya daya”, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013 take cika shakaru 10 da kafuwa. Da farko shawarar ta mayar da hankali ne kan zuba jari a fannin ababan more rayuwa, da ilimi, da gine-gine, da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata.
Alkaluma na nuna cewa, shawarar ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, wadanda suka taba rayuwar al’ummomi masu tarin yawa, musamman a kasashe masu tasowa da dama.
Shawarar “ziri daya da hanya daya” ta magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai da kuma kasashen Afirka.
Masana sun yi imanin cewa, duk da yadda wasu kasashen yammacin duniya suka yiwa shawarar bahaguwar fahimta, shawarar tana da muhimmanci wajen bunkasa alakar kasa da kasa. Kuma yanzu haka, akwai kasashe kimanin 140 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 28 da suka sanya hannu kan shawarar.
Saboda muhimmanci da tasirin da shawarar ke kara yi a sassan duniya, yanzu haka an sanya shawarar cikin muhimman takardun manyan hukumomin kasa da kasa misali, MDD, da kungiyar G20, da kungiyar raya tattalin arzikin Asiya da Fasifik da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da sauransu.
Bugu da kari, duk da sauye-sauye da yanayi na rashin tabbas da ra’ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra’ayi na kashin kai da duniya ke fuskanta a halin yanzu, shawarar da kasar Sin ta gabatar, wata dama ce da sauran kasashe za su amfana da irin ci gaba da ma fasahohin da kasar Sin ta samu.
Shawara ce da ke mutunta ra’ayoyi da ka’idojin kasashe da tuntubar juna da alaka ta samun nasara tare gami da nuna daidaito.
Bugu da kari, shawarar wani shiri ne da kasar Sin ta gabatar bisa buri guda da al'ummomin kasa da kasa ke da shi na samar da wadata ga duniya baki daya. A takaice dai shawarar “ziri daya da hanya daya” ta amsa sunanta da ma manufar kafata. (Ibrahim Yaya)