logo

HAUSA

Fu Qiaomei—— Matashiyar masaniyar kimiyyar kasar Sin wadda ta sake rubuta tarihin dan Adam na da

2023-07-18 09:41:09 CMG Hausa

A ranar 19 ga watan Yuni na shekarar 2023, a hedkwatar UNESCO da ke birnin Paris na kasar Faransa, aka shirya bikin karrama Fu Qiaomei, mai bincike a Cibiyar nazarin ilmin dabbobi da dan –Adam na da masu kashin baya ta Kwalejin Kimiyya ta kasar Sin da lambar yabo ta UNESCO- Abdullah Al Fozan ta kasa da kasa da aka kirkiro don kwararru matasa a fannonin kimiyya, fasaha, injiniya da lissafi, wato Abdullah Al Fozan a takaice, don nuna yabo kan mahimmancin aikinta, na gina tarihin gadon dabi’un halittan rukunin dan Adam na farko a babban yankin Turai da Asiya ta hanyar tsohuwar kwayar dabi’ar halitta, da sabbin fahimtar da ta kawo game da tambayoyi kan lafiyar dan adam da daidaitawa ta hanyar amfani da sauyin halitta.

Wannan lambar yabo ita ce lambar yabo ta farko ta kasa da kasa da UNESCO ta kafa tun shekarar 2022, don inganta ayyukan matasa masanan kimiyya a fannonin STEM, wato kimiyya, fasaha, injiniya da kuma lissafi, ana ba da lambar yabon ce bayan shekaru biyu ga matasa kwararru biyar da ke aiki a fannonin STEM, don gano da kuma ba da lada ga nasarorin da suka samu a matakan kasa, yanki da ma duniya wadanda ke ba da gudummawa ga habaka iya aiki, ciyar da ayyukan kimiyya gaba, da bunkasuwar zamantakewa da tattalin arziki, ta yadda za a karfafa aikin ba da ilmi, ci gaban kimiyya, yada ilmin kimiyya da kuma hadin kan kasa da kasa ta fuskokin STEM.

A matsayinta na daya daga cikin manyan masana kimiyya a fannin nazarin halittu na da na kasa da kasa, Fu Qiaomei ta yi fice daga cikin 'yan takara 2,500 na duniya wajen lashe wannan lambar yabo, kuma ta zama masaniya kimiyyar kasar Sin ta farko da ta samu wannan lambar yabo, hakan daga martabar kasar Sin a duniya a fannin kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha.

An haifi Fu Qiaomei, a watan Disamba na shekarar 1983, ta kuma fito ne daga gundumar Jiujiang ta lardin Jiangxi dake kudu maso gabashin kasar Sin. Ta gama makarantar sakandare ta lardin Jiujiang mai lamba 1 a watan Yuni na shekarar 2003, daga bisani ta shiga Jami'ar NorthWest don karanta fasahar Kariyar Kayan Al'adu. A shekara ta 2007, ta fara karatun digiri na farko a fannin kimiyya daga Jami'ar North West, sannan ba ta karbi tayin damar da makarantar ta ba ta na samun digiri na biyu ba tare da rubuta jarrabawa ba, a maimakon haka ta ci jarrabawar shiga Cibiyar kula da dalibai masu neman digiri na biyu ta Kwalejin kimiyya na kasar Sin don gudanar da bincike kan kasusuwa da abincin da dan Adam na zamanin da ke ci

A shekarar 2009, Fu Qiaomei ta sami digiri na biyu daga Cibiyar kula da dalibai masu neman digiri na biyu ta Kwalejin kimiyya na kasar Sin, a wannan shekarar kuma, ta tafi Cibiyar nazarin yadda halittu ta dan Adam ke sauyawa ta Max Planck da ke kasar Jamus don neman digiri na uku, inda a karkashin jagorancin masanin ilimin halitta kuma masani kan ilimin kwayoyin hallitar gado da yadda da suke rikida Svante Pbo, ta yi nazarin dabi’ar kwayar halittar dan Adam na zamanin farko. A shekarar 2013 kuma, ta samu digiri na uku a cibiyar ta Max Planck.

A halin yanzu dai Fu Qiaomei mai bincike ce, malamar dake koyar da dalibai masu neman digiri na uku, kuma darektar dakin gwaje-gwajen ilimin halittar jiki a Cibiyar nazarin ilmin dabbobi da dan-adam masu gashin baya na zamanin da ta Kwalejin Kimiyya ta kasar Sin.

Ta taba samun lambar yabo ta kwararrun matasan kasar Sin, da lambar yabo ta musamman ta fannin kimiyya da fasaha ta matasan kasar Sin, da lambar yabo ta kwararrun matasa mata, da lambar yabo ta matasan masana mata a fannin kimiyya ta kasar Sin da dai sauransu.

Tun tana karama, Fu Qiaomei ta kasance mai hazaka kuma mai sha'awar koyon ilmi, a shekarar 1998, ta kammala karamar sakandare, kuma ta samu gurbin karatu a makarantar koyar da malamai ta Jiujiang ta matsayi na uku a birnin Gongqingcheng. Sai dai bayan ta kammala karatu a makarantar a shekara ta 2001, ba ta zama malama ba, a maimakon haka sai ta ci gaba da zama daliba, wato ta zabi yin karatu a aji na biyu a Makarantar Sakandare ta 1 a gundumar Jiujiang. Domin ganin ta cimma babban burinta, tare da amincewar danginta, Fu Qiaomei ta yanke shawarar zuwa makarantar sakandare tare da yin jarrabawar shiga jami'a. Saboda wasu matsaloli kamar matsayin dalibi, ta taba zuwa makarantu da yawa, kuma a karshe makarantar ta karbi wannan daliba ta musamman.

Malam Duan Deming, babban malamin ajin Fu Qiaomei a makarantar Sakandare, har yanzu yana tuna cewa, saboda banbance-banbance da ke tsakanin manhajar karatun makarantar koyar da malaman koyarwa ta musamman da na sakandare, da kuma shiga aji na 2  na tsakiyar zangon karatu a makarantar, Fu Qiaomei ta fuskanci wahalhalu da yawa a farkon karatunta a makarantar sakandare. Amma ta magance matsalolin da ta fuskanta a farko bisa ga jajircewa da aiki tukuru da ta yi. 

Duan Deming, babban malamin ajin kuma malamin ilmin harhada sinadarai, ya yi tsokaci cewa, wani abu mai muhimmanci da fa'idar Fu Qiaomei shi ne "tana da himma da kokarin yin bincike", a kullum, za ta rubuta tambayoyi a littafinta don tambayar malamin. Lokacin da Chen Shangfa, malamin kimiyyar lissafi, ya tuna da wannan doguwar yarinya mai shiru da kwazo, ya kan ambaci musamman cewa tana "son yin tambayoyi kuma tana da kwazo da zurfin tunani". Malamin Turanci Shen Daohua ya ce game da wannan yarinya mai gaskiya da kunya, tana da rubutu mai kyau kuma tana yawan yin tambayoyi. Bisa namijin kokarinta, a jarrabawar rabin zangon karatu da aka yi bayan wata biyu, Fu Qiaomei ta samu matsakaicin maki a ajinsu.

A cikin wadannan watanni biyu kacal, Fu Qiaomei ta cimma nasarar koyon dukkan abubuwan da aka yi bata nan na tsawon shekaru uku, da sauran abubuwan da ba ta yi ba a shekarar farko ta sakandare.

To, masu sauraro, iyakacin shirinmu na yau ke nan, inda muka ba ku labari game da Fu Qiaomei, wadda ta lashe lambar yabo ta kasa da kasa ta UNESCO wato Abdullah Al Fozan da aka kirkiro don kwararrun matasa masana kimiyya a fannonin kimiyya, fasaha, injiniya da lissafi, wadda kuma ta kasance masaniyar kimiyyar kasar Sin ta farko da ta lashe wannan lambar yabo. Amma, wannan ba shi ne karshen labarin ba, a cikin shirinmu na makon gobe, za mu ci gaba da kawo muku bayani game da wannan baiwar Allah.