Kila manhajojin taimakawa yin barci za su taimakawa masu fama da matsalar yin barci
2023-07-18 09:35:21 CMG Hausa
Masu karatu, ko kun kasa yadda ya dace a rika yin barci da dare? An ruwaito cewa, wasu masu fama da matsalar yin barci sun fara yin amfani da manhajojin taimakawa yin barci, amma shin gaske ne wadannan manhajoji suna da amfani? Masu nazari daga kasar Birtaniya sun yi na’am da haka bayan wani dogon nazari.
Masu nazari da daga jami’ar Sussex ta kasar Birtaniya sun gayyaci masu aikin sa kai 300 don gudanar da wannan nazarinsu, inda suka tantance yadda wadannan masu aikin sa kai suke barci, da kimanta alakar da ke tsakanin barcinsu da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu. Masu nazarin sun bukaci wasu 180 daga cikin masu aikin sa kan su yi amfani da manhajar taimakawa yin barci, inda kafin su yi barci da dare, sun saurari amon muhallin dake kewaye da su, alal misali, yadda ruwan sama ke sauka, yadda ruwa ke gudu da dai sauransu, ko kuma sun saurari labarai kafin su yi barci.
Masu nazarin sun gano cewa, a lokacin da suka fara nazarinsu, matsakaicin tsawon lokacin da wadannan masu aikin sa kai suka dauka wajen yin barci da dare, ya kai awoyi 6 da mintoci 15. Bayan a kalla makonni guda 4 da suka fara amfani da manhajar, matsakaicin tsawon lokacin barcinsu ya karu da mintoci 30 a ko wane dare. Haka kuma tsawon lokacin da masu aikin sa kan su kan dauka wajen yin barci, ya ragu da kashi 1 cikin kashi 3, wato su kan dauki mintoci 20 ko fiye da haka kawai su fara yin barci. Ban da haka kuma, masu aikin sa kan sun kyautata gudanar da ayyukansu na yau da kullum bayan da suka huta sosai da dare, yayin da barazanar da suke fuskanta ta bakin ciki ko nuna damuwa, ta ragu.
Me ya sa haka? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, sauraron amo ko sautin dake muhallin dake kewaye da su ko labarai kafin yin barci, yana iya kare mutane daga damuwa da kuma samun matsin lamba, tare da sanya kwakwalwar mutane cikin nitsuwa, ta haka mutane suke samun saurin yin barci.
Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, idan nan gaba aka yi samun karin sakamakon tabbatar da lamarin, to, watakila manhajojin taimakawa yin barci za su yi kyakkyawan tasiri kan lafiyar al’umma. (Tasallah Yuan)