logo

HAUSA

Sharhi: Yadda Sin Ke Nisantar Da Duniya Daga Haɗari

2023-07-17 15:48:34 CMG HAUSA

 

Wasu ƙasashen yammacin duniya suna da ɗabi'ar ɗaiɗaikun ra'ayoyin da suka ƙirƙiro don biyan buƙatunsu na cikin gida. Misali na baya-bayan nan ya kasance kalmar "de- risking" wato “A guji haɗarin mu’amala da Sin”, wanda a hakikanin gaskiya "rarrabuwa" suke nufi, wannan ita ce da’awarsu asirce, dunkulewar duniya waje guda tamkar barazana ce a gare su. Duk wani mai hankali zai gane cewa wannan da’awar tasu, tsohon ruwan inabi ne kawai a cikin sabon kwalba.

 

Shekaru uku da suka gabata, ƙungiyar Eurasia, ɗaya daga cikin manyan masu ba da shawara kan haɗarin siyasa a duniya, ta kira "Tsarin Rarrabuwa ta Amurka" babbar haɗari dake fuskantar duniya. A maimakon mayar da hankali kan rikici cikin gidanta, Amurka ta zaɓi sanya wa wasu laƙabi da "haɗari" tare da zarge su da matsalolinta. Haɗarin Amurka a zahiri shi ke haifar da haɗari ga duniya, a yayin da ƙasar Sin ke nisantar da duniya daga irin wannan haɗarin.

 

Ƙasar Amurka na da dogon tarihi na aƙidar "wariya" tun daga lokacin da ta samu 'yancin kai. Gaskiyar ita ce: Amurka na kaucewa alhakin ƙasa da ƙasa da ke kanta, shi ya sa take shiga cikin cibiyoyi da yawa a daidai lokacin da yin hakan ya dace da son ranta. Yayin da take iƙirarin cewa ba ta da tsangwama kuma ba ta da hannu a cikin al'amuran wasu ƙasashe. Amurka na ci gaba da gina ƙananan ƙungiyoyi irin su AUKUS, QUAD, Five Eyes da G7 ɗauke da takamamman maƙasudi a cikin zuciya, da ya kunshi rarrabuwa, da adawa da rashin zaman lafiya.

 

Saɓanin haka, ƙasar Sin ta ƙuduri aniyar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil'adama, kuma ta tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya da aiwatar da tsarin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa tsawon shekaru da dama. Ta zama abokiyar tattaunawa ta ASEAN, da shiga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama, da ƙaddamar da bankin zuba jari na kayayyakin more rayuwa na Asiya, da ba da shawarwari ga jama'ar duniya. Da gabatar da shirye-shirye irin su shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya (BRI), da Shirin Ci Gaban Duniya, da Shirin Tsaro na Duniya da Tsarin Wayewar Duniya, da dai sauransu. Yayin da wasu ƙasashe suka janye daga wajibcin ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin da ƙungiyoyi, ƙasar Sin ta na ɗaɗa kira da a kara hadin kai, kuma ba ta taɓa yin watsi da nauyi da ke kanta  a matsayin babbar ƙasa ba.

 

"Dala ita ce kudinmu, amma matsala ce gare ku." Wannan sanannen ƙa’ida ce a Amurka. Tsawon shekaru, a ƙarƙashin mulkin dala, Amurka ta haddasa hauhawar farashin kayayyaki ga sauran ƙasashen duniya, ta haifar da rikicin kuɗi da na bashi a wasu ƙasashe da kuma kara haɗarin tattalin arziki da kuɗi na ƙasa da ƙasa. Ta ci gaba da yin amfani da rinjayen dala don yin "ta'addanci na kuɗi." Ta kakkaba wa ƙasashe kusan 40 takunkumin tattalin arziki, lamarin da ya yi illa ga kusan rabin al'ummar duniya. Bugu da ƙari, Amurka tana yin amfani da fa'idodinta na fasaha ta hanyar gina "ƙananan dandali masu manyan shinge" kamar "Chip 4 alliance" da "Clean Network initiative" – wanda har abokan hulaɗarta ba za su amfana da waɗannan shirye-shiryen ba.   

 

Ƙasar Sin, ba kamar Amurka ba, tana da ikon samun wadata kuma tana baiwa sauran ƙasashen duniya damar ci gaba a cikin wadatar da ta samu. Tare da halartar ƙasashe 150 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 30, BRI ta samar da ayyukan haɗin gwiwa sama da 3,000, da samar da ayyukan yi na kusan 420,000, tare da fitar da kusan mutane miliyan 40 daga kangin talauci. Layin dogo na Mombasa-Nairobi, da layin dogo na kasar Sin zuwa Laos da babban layin dogo na Jakarta-Bandung sun kawo ci gaba na gaske ga al'ummomin yankin. Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin wato CIIE, ya kasance wani dandali mai inganci ga kamfanoni a duk duniya, don cin gajiyar ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin.

 

Kamar yadda Jeffrey Sachs, farfesa kuma darektan cibiyar raya ci gaba mai dorewa ta jami'ar Columbia, ya ce a dandalin dimokuradiyya na Athens 2022, kasar Sin ta samu nasarori masu ban mamaki a cikin shekaru 40 da suka gabata, don haka ya kamata mu "yi farin ciki da nasarorin da ƙasar Sin ta samu, ba wai mu tsorata ba."  (Yahaya)