logo

HAUSA

Kyan Wayewar Kai Na Cikin Bambance-Bambancen Dake Akwai Tsakaninsu

2023-07-16 20:49:58 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A kwanakin baya, a yayin da al’ummar musulmi a sassan duniya suka yi shagulgulan babbar sallah, wani abu da ya faru a Turai ya bata yanayin bikin, inda bisa amincewar ’yan sandan wurin, an sake samun wani da ya kona Alkur’ani mai tsarki a wajen wani masallacin da ke birnin Stockholm, babban birnin kasar Sweden.

Bayan aukuwar lamarin, firaministan kasar ta Sweden Ulf Kristersson ya bayyana cewa, duk da cewa lamarin bai dace ba, amma ba a karya doka ba. Shi kuma kakakin majalisar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya furta cewa, Amurka na goyon bayan ’yancin jama’a na fadin albarkacin baki, kasancewarsa wani bangare na dimokuradiyya. Sai kuma babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg da ya ce, wannan na daga cikin ’yancin jama’a na fadi albarkacin bakinsu. Lallai irin matsayin da kasashen yammacin duniya suka dauka ya jawo suka daga gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashen musulmi.

Dangane da aukuwar lamarin, daga ranar 11 zuwa 12 ga wata, an gudanar da muhawara ta gaggawa a gun taron majalisar kula da hakkin dan Adam ta MDD karo na 53, inda zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD da ke Geneva ya yi Allah wadai da aukuwar lamarin da kakkausar murya, ya ce, a kullum kasar Sin na ganin cewa, ya kamata a yayata akidar martaba juna, da tafiya tare da dukkanin sassa, da koyi da juna tsakanin mabanbantan al’ummu, kuma tana tsayawa tsayin daka a kan kin yarda da nuna kyamar musulunci.

Lamarin da ya faru a kasar Sweden ba shi ne karo na farko ba. A cikin ’yan shekarun baya, a yayin da ake ta kara samun rikici a tsakanin sassan duniya, wasu ’yan siyasar kasashen yammacin duniya na ta kara tunzura fito na fito tsakanin al’ummu da wayewar kansu. Idan ba a manta ba, mujallar Charlie Hebdo ta Faransa ta sha wallafa zanen barkwanci da suka tada sabani a tsakanin addinai da kabilu daban daban. Tun daga watan Agustan shekarar 2020, sau da dama, wasu tsirarrun ’yan siyasar Turai sun kona Alkur’ani mai tsarki a fili. A watan Janairun shekarar 2017, gwamnatin kasar Amurka ta kaddamar da dokar kayyade shigar da al’ummar kasashen musulmi kasar, matakin da ya sa ta zama kasa daya tilo a duniya da ta sanya haramci kan rukunin al’ummar musulmi. Duk wadannan lamura sun tunzura kiyayya a tsakanin mabambantan al’ummu, tare da tsananta rashin fahimtar juna a tsakanin kabilu daban daban, kuma ainihin dalilin da ya sa haka shi ne yadda kasashen yammacin duniya ke nuna bambanci ga irin al’ummun da ba nasu ba, wadanda a ganinsu, wayewar kai na yammacin duniya ya fi na sauran sassan duniya.

Kasar Sin a nata bangaren, tana ganin cewa, duk da bambance bambance da ke tsakanin wayewar kai iri iri, amma babu wani da ya fi wani na daban, don haka ma, kullum take kira da a kiyaye kasancewar mabambantan wayewar kai, tare da sa kaimin yin musaya a tsakaninsu. Kuma hakan ya faru ne sakamakon yadda kasar Sin ta kasance kasar da ke da kabilu da dama tun fil azal, wadanda suka yi ta zaman cude-ni-in-cude-ka a tsawon tarihi na kasar, a yayin da kuma suka yi ta yin musayar wayewar kansu tare da samun ci gaba tare. Baya ga haka kuma, addinai da dama, ciki har da addinin Buddah, da Musulunci da Kirisita duk sun shigo nan kasar har sun samu bunkasa sun zama muhimman bangarori na wayewar kan kasar Sin.

Sabo da irin wannan akidar martaba mabambantan wayewar kai da kasar Sin ke da shi, a watan Maris na wannan shekara, kasar ta gabatar da shawarar bunkasa wayewar kai tsakanin al’ummun kasa da kasa, inda ta yi kira da a aiwatar da manufofin daidaito, da koyi da juna, da tattaunawa, da tafiya tare tsakanin dukkanin wayewar kan al’ummun duniya.

Wayewar kan musulunci ta bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban duniya, kuma an sha yin musaya a tsakanin wayewar kan al’ummar kasar Sin da na musulunci, matakin da ya zama misali na yin musaya a tsakanin wayewar kai daban daban. Kawo yanzu, kasar Sin da kasashen musulmi sun gudanar da taron kara wa juna sani game da wayewar kan juna har sau hudu. A ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2022 kuma, kasar Sin ta sa kaimi ga taron MDD ya zartas da kudurin tsai da ranar 15 ga watan Maris na kowace shekara a matsayin “ranar duniya ta adawa da kyamar musulunci”.

Kasancewar bambance-bambance dake tsakanin wayewar kai daban daban, shi ya sa suke yin musaya a tsakaninsu, kuma sabo da irin musaya ne, ake samun ci gaba na bai daya, don haka muke cewa kyan wayewar kai na cikin bambance-banbancen dake akwai tsakaninsu. Muna fatan kasa da kasa za su hada hannu su yayata shawarar bunkasa wayewar kai tsakanin al’ummun kasa da kasa, don kiyaye mabambantan wayewar kan al’ummmun duniya. A sa’i daya kuma, muna fatan wasu kasashen yamma za su dauki matakai, don daidaita ainihin matsalolin nuna bambanci, kuma su karfafa fahimtar addinai da wayewar kai da ba irin nasu ba. (Lubabatu Lei)