logo

HAUSA

Ziyarar firaministan kasar tsibiran Solomon a kasar Sin tana da babbar ma’ana ga kasar

2023-07-15 16:43:29 CMG Hausa

Yayin ziyararsa a kasar Sin a ranar 13 ga wannan wata, Firaministan kasar tsibiran Solomon Manasseh Sogavare, ya je lardin Jiangsu na kasar Sin, inda ya ziyarci kauyen Huanglongxian, mai tarihin al’adun shayin. Yayin ziyarar, firaministan ya gano yadda wannan kauye ya kawar da talauci ta hanyar amfani da albarkatun halittu da shuke-shuken shayi, lamarin da ya bayyana a matsayin misali da kasarsa ka iya koyi da shi.

Wannan shi ne karo na biyu da firaminista Sogavare, ya ziyarci kasar Sin tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da kasarsa a shekarar 2019.

Bugu da kari, yayin ziyarar, kasashen biyu sun kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni bisa girmama juna da samun bunkasuwa tare a sabon zamani.

A gun taron koli karo na farko na dandalin tattaunawar hadin gwiwa don samun ci gaban duniya da aka gudanar a birnin Beijing, Sogavare ya bayyana cewa, ana bukatar raya ayyukan more rayuwa masu inganta karfin tattalin arziki don kawar da talauci, kuma kasar Sin, abokiya ce mafi girma ga kasar tsibiran Solomon a wannan fannin. Yanzu, dakin wasannin motsa jiki da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa domin gasar wasannin motsa jiki ta yankin tekun Pasifik ta shekarar 2023 a Honiara, babban birnin kasar tsibiran Solomon, ya riga ya kasance wata alama ta birnin.

Har ila yau a yayin ziyarar firaminista Sogavare, kasashen biyu sun daddale yarjejeniyoyi da dama dake shafar fannonin samun bunkasuwa, da cinikayya, da zirga-zirgar jiragen sama, da kwastam, da yanayi da sauransu, ta yadda za a zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu. Kana an sada zumunta tsakanin lardin Guangdong da jihar Guadalcanal, da kuma tsakanin birnin Jiangmen da birnin Honiara, lamarin da zai fadada hadin gwiwar dake tsakanin kwamitocin tsakiya na kasashen biyu da kuma tsakanin hukumomin wuraren kasashen biyu, tare da kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin jama’arsu. (Zainab)