logo

HAUSA

Gidan yari da Amurka ta kafa a ketare ya keta hakkin bil Adama

2023-07-14 10:50:31 CMG HAUSA

DAGA MINA

Kwanan baya, wakilin musamman na MDD ya kai ziyara a gidan kurkuku na Guantanamo, inda ya gano cewa, an yi wa mutane da aka tsare a wurin azaba. A cikin shekaru da dama da suka gabata, Amurka ta kafa gidajen kurkuku a wurare daban-daban a duniya inda ta fake da batun yaki da ta’addanci. Alkaluma da aka fidda sun nuna cewa, bayan batun “9.11”, wadannan gidajen kurkuku sun shafi kasashe ko yankuna fiye da 54, inda aka tsare mutane fiye da dubu 10, ciki har da musulmai da mata da yara da sauransu, har an yiwa fursunonni azaba.

Ofishi mai kula da harkokin kasa da kasa da al’umma na jami’ar Brown na Amurka ya taba ba da wani rahoto cewa, mutanen da Amurka ta tsare a wadannan gidajen kurkuku a matsayin ‘yan ta’adda, babu shaidu dake bayyana cewa, wadannan mutane ‘yan ta’adda ne, kuma ba a taba kai su kotu ba. Ban da wannan kuma, ‘yan sanda sun yi musu azaba, matakin da ya illata jiki da ma zuciyar mutanen.

Amurka tana tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe bisa ikirarin demokuradiyya da kare hakkin bil Adam, abin da ya keta dokar kasa da kasa. Ya kamata Amurka ta rufe wadannan gidajen kurkuku da yin nadama kan laifukan da ta aikata, da ma rokon gafara da biyan diyya da gurfanar da wadanda suka yiwa mutane azaba a gaban kotu. (Mai zana da rubuta: MINA)