logo

HAUSA

Shin Amurka na son maimaita laifukan da ta aikata a kan al'ummar Laos a rikicin Ukraine?

2023-07-14 11:01:23 CMG Hausa

Tawagar injiniyoyi sun shafe fiye da shekaru biyu, suna aikin share bama-bamai masu ’ya’ya da Amurka ta bari, kafin a yi nasarar gina layin dogo tsakanin Sin da Laos. Sojojin Amurka ne suka jefa wadannan bama-bamai a Laos a lokacin yakin Vietnam.

A kwanakin baya gwamnatin Amurka ta sanar da cewa, za ta baiwa Ukraine karin tallafin soji da darajarsu ya kai dalar Amurka miliyan 800, ciki har da bama-bamai masu jigida da dokar Amurka ta haramta amfani da su.

Bayan barkewar rikicin Ukraine, Amurka ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin makamai da alburusai daban-daban. Amma bayan da Amurka ta sanar da baiwa Ukraine bama-bamai masu ’ya’ya, firaministan Burtaniya Rishi Sunak ya ce, Burtaniya na daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa da ta haramta amfani da wadannan bama-bamai, kuma ba ta karfafa yin amfani da irin wadannan makamai. Haka ma kasashen Spain, da Canada da sauran kasashe sun nuna adawarsu kan wannan mataki.

A shekarar 2008, gwamnatin Amurka ta yi alkawarin tabbatar da cewa, sojojin Amurka ba za su sake yin amfani da irin wadannan bama-bamai masu ’ya’ya ba, kuma za su kawar da duk wani nau’i na wadannan makami. Sai dai kuma, makaman da aka aikawa Ukraine a wannan karo, bama-bamai ne masu ‘ya’ya, da aka samar fiye da shekaru 40 da suka wuce, kuma aka haramta amfani da su shekaru 15 da suka gabata.

Bugu da kari, wani abin mamaki shi ne, shekarar da ta gabata, Sakatariyar yada Labarai ta Fadar White House ta Amurka, Jen Psaki, ta ce idan aka yi amfani da bama-bamai masu ’ya’ya, tamkar aikata laifukan yaki ne. Shekara guda bayan haka, ana iya cewa, Amurka ta zama mai la’antar kanta da kanta. (Ibrahim)