Baba Ahmad Jidda: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Zurfafa Zumuncin Da Ke Tsakanin Sin Da Afirka
2023-07-14 20:04:21 CMG Hausa
Jakadan Najeriya a kasar Sin Baba Ahmad Jidda ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya ta zurfafa dankon zumunci a tsakanin kasar Sin da Najeriya da kuma tsakanin Sin da kasashen Afirka, yana mai cewa Najeriya na sa ran samun karin damammakin bunkasuwa daga aiwatar da shawarar.
Jakadan ya bayyana haka ne yayin da ya zanta da wakiliyar CMG a kwanan baya, inda ya bayyana cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, muhimmiyar shawara ce da kasar Sin ta gabatar domin kara azama kan samun ci gaba tare da wadatar da kowa. Ya ce a matsayinta na dandalin hadin gwiwa da ke bude kofa ga kowa, shawarar ta amfana wa kasashen Afirka da zurfafa dankon zumunci a tsakanin kasar Sin da Najeriya da kuma tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Ya ce tun bayan da Najeriya ta shiga shawarar a shekarar 2018, kasashen Sin da Najeriya sun kyautata hadin kansu a sassa daban daban. Kuma sun samu sakamako da yawa a fannonin raya ababen more rayuwa da zuba jari kan masana’antu. A watan Yunin bana, jakadan ya ziyarci kamfanin CRRC a lardin Jiangsu, wanda ya samar wa Najeriya jiragen kasa masu inganci. Jakadan ya bayyana cewa, al’ummar Najeriya suna son jiragen kasan, wadanda suke da inganci, da dadin zama, yana mai cewa zai ci gaba da kara azama kan hadin gwiwar kasashen 2 a fannoni masu ruwa da tsaki. (Tasallah Yuan)