logo

HAUSA

Sin Na Cika Alkawuranta Na Hadin Gwiwar Raya Kiwon Lafiya Ga Kasashen Afirka

2023-07-13 16:02:24 CMG Hausa

A karshen makon jiya, tawagar tallafin kula da lafiya ta kasar Sin mai aiki a kasar Zambia, ta tallafawa asibitin koyarwa na jami’ar Levy Mwanawasa dake birnin Lusaka, da kayayyakin aiki da darajarsu ta kai kimanin dalar Amurka dubu 28, matakin da mahukuntan Zambia suka ce ya zo kan gaba, ganin yadda asibitin ke bukatar irin wannan taimako.

Wannan dai irin tallafi da Sin ke samarwa a kai a kai ga kasashen Afirka daban daban, bangare ne na irin alkawura da mahukuntan Sin din suka sha nanatawa, game da burinsu na karfafa kawance da hadin giwa, da goyon bayan juna tare da abokan tafiya na kasashen Afirka.

An dai sha jin mahukuntan kasar Sin na jaddada cewa, za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun bunkasa kawance da hadin kai da kasashe masu tasowa, ciki har da na nahiyar Afirka, wadanda har kullum ke goyawa Sin din baya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Bisa wannan fahimtar juna da matakai daban daban na cika alkawura, kawo yanzu gwamnatin kasar Sin ta aike da tawagogin likitoci masu aikin ba da tallafin kiwon lafiya na Sin 24, da na sojoji jami’an lafiya 45 zuwa Zambia, jimillar adadin da ya kai likitoci da kwararru a fannin kiwon lafiya 993, wanda hakan ya tabbatar da sahihancin wannan manufa ta marawa kasashen Afirka baya a fannin kiwon lafiya da Sin din ke aiwatarwa.

Ko shakka babu, irin wannan tallafi da tawagogin kiwon lafiya na Sin ke aiwatarwa a Zambia da sauran kasashen Afirka, shi ne abun da nahiyar ta fi bukata a fannin habaka kawance, da cimma moriyar juna, sabanin cacar baka, ko kafa wani kawance domin ware wani bangare, ko cimma bukatu na siyasa. (Saminu Alhassan)