logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ke kokarin samun ci gaba tare da ragowar kasashen duniya

2023-07-12 08:28:19 CMG Hausa

A kwanakin baya ne aka gudanar da taron koli na farko na manyan jami’an dandalin tattaunawa kan samun ci gaba tare na kasa da kasa. Wannan ne ma ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga wannan muhimmin biki.

A cikin wasikar tasa Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu duniya na fuskantar manyan sauye-sauye, kana an fuskanci matsaloli da dama yayin farfado da tattalin arzikin duniya, haka kuma ajandar ci gaban duniya tana fuskantar kalubale. 

Shugaba Xi ya kuma gabatar da shawarar raya duniya, ta yadda za a gaggauta aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samu ci gaba tare.

Ya ce, yana farin cikin ganin irin sakamako da aka fara samu a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar, har ma kasashe masu tasowa da dama sun fara cin gajiyar hakan.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara zuba jari a fannin hadin gwiwar kasa da kasa, da yin aiki tare da sauran kasashen duniya domin taka rawa wajen tabbatar da ganin ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030 ta kai ga nasara, tare da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil Adama. Kadan daga fannonin samun nasara tare da Sin ta gudanar a sassan duniya, sun hada da madatsar ruwa da wani kamfanin kasar Sin ya gina a kasar Mauritius, matakin da ya taimaka wajen kawo karshen matsalar ruwan sha da birnin ke fuskanta.

Akwai kuma layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi na kasar kenya, da kananan kwasa-kwasai da kasar Sin ta shiryawa maluman gona da masu dashen itatuwa da kare muhalli na Afirka a lokuta daban-daban da ma sauran fasahohin samun ci gaba da sauransu. Wadannan da ma wassu, sun kara nuna yadda Sin ke kokarin samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya ba kuma tare da gindaya wasu sharudda ba. (Yahaya, Ibrahim /Sanusi Chen)