logo

HAUSA

NATO ta yi kuskure kan fatan “ci gaba da dorewa” ta hanyar wargaza yankin Asiya da Pasifik

2023-07-12 11:18:16 CMG Hausa

Kungiyar tsaro ta NATO ta fara gudanar da taron kolin ta jiya Talata a kasar Lithuania. Baya ga babban jigon taron game da halin da ake ciki a kasar Ukraine, shugabannin kasashen Japan, da Koriya ta Kudu, da Australia, da New Zealand sun halarci taron a karo na biyu a jere, lamarin da ya sa batun samar da zaman lafiya na kungiyar NATO ya sake yin zafi. Kafofin yada labaran kasar Japan sun bayyana cewa, sakamakon adawar kasar Faransa, aka dage shirin bude ofishin hulda da kungiyar NATO na farko a yankin Asiya a kasar Japan, wanda tun da farko aka tattauna a taron kolin, har sai bayan kaka. Sai dai manazarta na ganin cewa, a karkashin jagorancin Amurka, aniyar kungiyar NATO ta fadada ikonta zuwa yankin Asiya da tekun Pasifik ba za ta canja ba.

A matsayin wani samfuri na zamanin yakin cacar baka, NATO ta kasance ginshikin tabbatar da mulkin Amurka tun kafuwarta. Tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka, kungiyar NATO ta fadada ikonta zuwa gabashi har sau shida bisa dabarun Amurka na "taimakawa Jamus da Faransa", "da mayar da Rasha saniyar ware" da "gasa da kasar Sin ", wanda ya tada rikici tsakanin Rasha da Ukraine, da haifar da rarrabuwar kawuna a Turai, kuma tana ci gaba da fadada tasirinta zuwa yankin Asiya da Pacifik.

Yankin Asiya da Pacifik yanki ne mai fadi don neman hadin kai da ci gaba, ba kuma fagen da manyan kasashe za su yi gasa ba ne. Kungiyar NATO da Amurka ke jagoranta, tana son maimaita abin da ake kira "Kwarewar Turai" zuwa yankin Asiya da Pasifik, amma a hakikanin gaskiya, tana son kara haifar da rarrabuwar kawuna da rikici da yankin, amma jama’ar yankin ba za su yarda ba. NATO tana son "ci gaba da dauwama" ta hanyar wargaza yankin Asiya da tekun Pasifik, kuma mutane masu son zaman lafiya a fadin duniya ba za su taba yarda ba. Kamar yadda Ken Stone, shugaban kungiyar da ke adawa da tayar da yaki ta kasar Canada, ya ce, NATO kungiya ce mai karfin fada-a-ji da Amurka ke jagoranta, bisa ga tsarin dokokin kungiyar, ta dade da yin hannun riga da ma'anar kafa ta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)