logo

HAUSA

Hakkin Makwabtaka Muhimmin Abu Ne Da Ya Kamata Japan Ta Yi La’akari Da Shi

2023-07-11 16:07:32 CMG Hausa

Yayin taron hukumar kare hakkin bil adama ta MDD karo 53 dake wakana, kasar Sin ta sake kira ga Japan da ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku.  Ko a makon da ya gabata, kasar Sin ta yi irin wannan kira,  tana cewa bai kamata Japan ta dauki rahoton IAEA a matsayin izini aiwatar da nufin nata ba.

Ba yanzu kasar Sin da sauran kasashe makwabta suka fara bayyana damuwa dangane da wannan batu ba, lallai ya zama wajibi Japan ta sake nazari game da kudurin nata don ganin ba ta sa son rai a ciki ba. Hakkin makwabtaka babban abu ne, domin a ko da yaushe, makwabta ne ke iya kai dauki na farko-farko idan bukatar hakan ta taso, haka kuma babu wanda zai iya tserewa duk wata annoba da za ta shafi makwabcinsa. Kamata ya yi Japan ta yi nazari, ta kuma duba korafin makwabtanta domin suna da hakki a kanta, kana ta yi la’akari da wasu al’ummominta da su ma suke adawa da matakin nata.

Idan Japan ta yi gaban kanta tare da biyewa kasashe masu hure mata kunne, lallai mummunan tasirin abun da za ta aiwatar ba zai tsaya kan makwabtanta ba, ita kanta za ta dandana kudarta, don haka, gudun kar a yi, to kar ma a fara.

Kamar yadda kasar Sin ta bayyana, bai kamata Japan ta dauki rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta fitar a matsayin izinin zubar da dagwalon nukiliya cikin tekun ba, domin alamomi sun nuna cewa, an yi gaggawar fitar da rahoton, kana ba a sanar da dukkanin masanan da suka yi nazarin sakamakon ba. Ko kadan gaggauta fitar da rahoto game da muhimmin batu irin wannan bai dace ba, kuma ba zai haifar da da mai ido ba, domin akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi la’akari da su duba da cewa, ya shafi al’ummomi da dama.  

Abu mafi dacewa shi ne, Japan ta dakatar da shirin, ta hada kai tare da tuntubar masana daga kasashen makwabtanta da ma hukumar IAEA, domin sake gudanar da nazari wanda zai kasance bisa gaskiya da adalci da ilimi, su daddale, su lalubo mafita mafi dacewa da za ta karbu ga dukkan bangarori, ba tare da cutar da wani ba, haka kuma wadda za ta dore. Kana, Japan ta daina sauraron zugar kasashen yamma wadanda kansu kadai suka sani, kana ba su da masaniya ko ma ba su damu da yanayin da shirin zai iya jefa al’ummar yankin ba.  (Fa’iza Mustapha)