Mataimakin gwamnan Jigawa a Najeriya ya bayyana fatan kara inganta hadin-gwiwa tare da Sin
2023-07-11 15:08:27 CMG Hausa
Mataimakin gwamnan jihar Jigawa dake arewacin Najeriya, Malam Aminu Usman Yakubu, ya halarci bikin baje-kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na uku, wanda ya gudana a birnin Changsha na lardin Hunan. Kaza lika ya halarci wasu muhimman tarukan bikin, ciki har da dandalin tattaunawa kan inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin raya muhimman ababen more rayuwar al’umma, tare da gabatar da jawabi.
Wakilin mu Murtala Zhang, ya samu damar zantawa da mataimakin gwamnan, wanda ya ce a halin yanzu, akwai hadin-gwiwa da mu’amala mai karfi tsakanin jihar Jigawa da kasar Sin, a fannonin da suka shafi hako ma’adinai, da inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da ayyukan noma da sauransu. Kuma ta hanyar halartar baje kolin na wannan karo, yana fatan karfafa hadin-gwiwa tsakanin jiharsa da Sin, musamman a fannin aikin gona da wutar lantarki.
Mataimakin gwamnan, ya kuma bayyana kokarin da sabuwar gwamnatin jihar Jigawa za ta yi, domin kyautata rayuwar al’ummar ta. (Murtala Zhang)