Ya dace Amurka ta dauki hakikanin matakai domin karfafa hadin gwiwa da Sin
2023-07-10 10:18:09 CMG Hausa
Jiya ne, sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen ta kammala ziyararta ta kwanaki hudu a kasar Sin. Yayin shawarwarin da sassan biyu suka yi lokacin ziyararta, Sin da Amurka sun nuna aniyarsu ta kara karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakaninsu. Jami’an kasar Sin sun jaddada cewa, matakin da bangaren Amurka ya dauka ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa zai kawo cikas ga huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, A nata jawabin, Yellen ta sake bayyana cewa, kasarta ba ta son rabuwa da kasar Sin a bangaren tattalin arziki, kuma ta yi alkawari cewa, za ta yi kokarin kyautata hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasarta da kasar Sin domin samun moriya tare.
Yellen, ita ce babbar jami’ar gwamnatin Amurka ta biyu da ta kawo ziyara kasar Sin a cikin wata guda. Kafin wannan, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ziyarci kasar Sin. Bisa bayanan da bangarorin biyu suka fitar, ziyarar Yellen a wannan karon ta baiwa kasashen Sin da Amurka damar kara fahimtar damuwar juna, kana bangarorin biyu sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa.
Amma an lura cewa, Yellen tana ci gaba da bayyana wasu manufofin Amurka da ba su dace ba bisa fakewa da batun tsaron kasa, inda ta sanar da cewa, za ta tsara wani tsarin tattalin arziki mai adalci. Bangaren kasar Sin shi ma ya nuna damuwa kan takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Sin. Masu sharhi sun yi nuni da cewa, har yanzu akwai bambance-bambance a tsakanin Sin da Amurka ta fuskar inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, musamman ma cewa har yanzu ya dace Amurka ta kara kokari.
Bayan Yellen ta koma kasarta, ana sa ran gwamnatin Amurka za ta dauki hakikanin matakai domin ciyar da huldarta da kasar Sin gaba yadda ya kamata. (Jamila)