logo

HAUSA

Jiang Xiaoxi: Direba mai kokarin aikin jigilar abinci

2023-07-10 15:22:54 CMG Hausa

“Babu wani abu na al’ajabi, hazaka ce da jajircewa kadai. Kana iya rashin sa’a, amma kada ka cire tsammani. Gumi kamshin nasara ne.” Wadannan kalamai ne da Jiang Xiaoxi, ‘yar kasar Sin ta wallafa a shafinta na manhajar WeChat. Jiang Xiaoxi mai shekaru 23, direba ce mai aikin jigilar abinci kuma shugabar wata tashar masu aikin jigilar abinci dake karkashin kulawar dandalin bayar da hidima ta intanet mai suna Meituan, a yankin Bao’an na birnin Shenzhen a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. Jiang wadda ita ce shugaba irinta mafi kankantar shekaru a Shenzhen, na jagorantar direbobin jigilar abinci sama da 30, wadanda ke shiga lungu da sako na unguwar Shajing domin hidimtawa mazauna.

Da misalin karfe 10:30 na wata rana, yayin hutun bikin Bazara na shekarar 2023, Jiang ta samu odar kai abinci na farko. Ta samu odar ne daga manhajar Meituan. Nan da nan ta tsara hanyar da za ta bi, ta daure hular kwanon dake kanta, ta fara aikinta a ranar a kan babur dinta na lantarki. Galibin abokan aikin Jiang sun koma garuruwansu domin haduwa da iyalansu, amma Jiang ta zabi ta yi aiki yayin hutun.

A shekarar 2018, Jiang ta koma Shenzhen daga garinsu wato Shaoyang dake lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin. Cikin lokaci kalilan ta zama direba mai jigilar abinci ga Meituan. “Idan dai kana da hazaka kuma za ka iya yin aikin da kyau, to za ka iya samun sama da yuan 10,000 (kwatankwacin dala 1,428) a wata. Kasancewar mahaifiyarta ba ta da lafiya, da dan uwanta dake makaranta, tana bukatar samun kudi domin taimakawa mahaifinta kula da iyalin.

Nan da nan ta fahimci cewa, aikin na bukatar fasahohi ba tukin babur ba kadai. “oda na iya kai ka ko ina, ana bukatar jarumta wajen shiga kowanne lungu na birnin,” cewar Jiang.

Wani lokaci, wasu abubuwa mara dadi kan auku. A wata rana, wani kwastoma ya taba neman a kai masa abinci gidansa, amma sai ya yi kuskure wajen sanya adireshi. Sai bayan ta isa wurin, ta kira shi, sannan suka gane an yi kuskure. Sai ta ce za ta kai masa abincin, amma sai bayan mintuna 20 saboda tana da wasu oda na gaggawa da za ta kammla tukuna. Amma kwastoman bai yaba mata ba, inda ya nemi lallai ta kai masa abinci kan lokaci. Duk da ba ta ji dadi ba, ta yi kokarin kai masa abincin kamar yadda ya bukata.

Jiang ta hadu da kwastomomi iri-iri, sai dai, ta fi tuna wadanda suka yi mata kirki. Jiang ta ce,“dukkan kyautatawa komai kankantarsa na nuna min cewa, akwai mutane da dama da suka fahimta tare da yabawa ayyukanmu. Kuma wannan ya ba ni kwarin gwiwar ci gaba da wannan aiki.”

A wata rana, ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, oda sun yi wa direbobi yawa, har aka dakatar da odar wani kwastoma, saboda babu direban da ya karbi odar. Sai Jiang ta yi ta maza ta yanke shawarar kai masa odar. Amma an samu jinkiri sosai, don haka ta yi ta ba shi hakuri saboda ta dauka ya yi fishi. Sai dai, bai yi korafi ba, maimakon haka, sai ya ba ta kyautar madara da kuki. “a wannan lokaci, hawaye ya cika a idona,” cewar Jiang.

A shekarar 2019, yayin hutun bikin bazara, wani kwastoma dake zaune a hawa na 6, na wani ginin da babu lifta, ya yi odan abubuwa da dama. Sai da Jiang ta hau matakala sau biyu domin kai masa kayayyakin. Tana haki ta ce masa “barka da sabuwar shekara” ta juya ta tafi. Nan ba da jimawa ba, ta ga wayarta ta yi haske, sai ta ga sako daga manhajar Meituan, wanda ke nuna cewa ta samu kyautar kudi har yuan 199 (kwatankwacin dala 28) daga wannan mutumin. Wannan sa’ar sabuwar shekara ce a gare ta, da kuma yabawa hazakarta, wanda ya faranta mata rai matuka.

A farkon shekarar 2022, an samu barkewar annobar COVID-19 a birnin Shenzhen, inda aka rufe unguwanni da dama. Masu aikin jigilar kai sakwanni sun gudanar da muhimmin aiki ta hanyar jigilar abinci da magunguna da sauran kayayyaki, domin taimakawa mutane tafiyar da rayuwarsu. Sun kuma tabbatar da harkoki sun ci gaba da gudana a birnin.

Jiang ba ta dauki ranar hutu ko da sau daya ba, maimakon haka, ta jagoranci tawagarta wajen yin iya kokarinsu na kammala kai oda. Jiang ta ce, “Ba za a hada aikinmu da na jami’an lafiya da sauran masu yaki da annobar ba, amma mun yi farin cikin bayar da tamu gudunmuwa.”

Baya ga kai abincin da aka yi oda daga dakunan cin abinci, mutane kan yi odar kayayyakin masarufi da suka hada da hatsi, man girki, ‘ya’yan itatuwa da kayayyakin lambu. Jiang ta ce, “wata uwa na bukatar wani nau’in madarar yara cikin gaggawa. Na damu kada danta ko yarta su yi fama da yunwa, don haka na je shaguna daya bayan daya har sai da na samo.” Wannan uwa ta yi mata godiya matuka, wanda ya farantawa Jiang rai. “Ina son yin bakin kokarina wajen taimakawa mutane,” cewarta.

Aiki a matsyain mai kai abinci a Shenzhen, ya taimakawa Jiang samun karin kwarin gwiwa kuma ta kulla alaka da birnin da ma jama’arsa. Jiang ta ce, “ina son wannan aikin, kuma ina son yin rayuwa mai kyau a nan.”

Jiang Xiaoxi ta kan shafe lokaci mai tsawo tana aiki, fatarta ta yi duhu kuma jikinta ya kara karfi idan aka kwatanta da sauran ‘yan mata sa’anninta. Yanayin jikinta da halayyarta suka sa abokan aikinta ke kiranta da “Babban yaya”.

A ko da yaushe, cike Jiang take da kuzari, ta kan kai sakwanni har kusan 100 a rana guda. Kuma ita ce ta zo ta daya cikin masu aikin kai sakwanni a Shenzhen, a fannin adadin odar da ta kai. Abokan aikinta na alfahari da ita, inda suke kiranta da “Sarauniyar kai sakwanni ta yankin Shajing”.

Jiang ta kasance tamkar taswirar Shajing mai rai, saboda ta san lungu da sako dake da nisan kilomita 10 daga wurin kai sakwanni. “idan aka tambaye ni kwatancen wuri, to amsata ta fi ta manhajar taswirar nuna hanya,” cewarta.

Idan direba na son kammala kai sakwanni masu yawa, ya kamata ya san hanya sosai. A cewar Jiang, wannan fasaha ce mai muhimmanci. Jiang kan tsara hanyar da ta fi sauri, kuma ta kammala kai oda da yawa, fiye sauran direbobi. A lokacin da ba ta aiki, Jiang kan yi yawo a kan tituna da lunguna, tana tuna lambobin gidaje da gano gajerun hanyoyi domin taimaka mata tsara yadda za ta kai sakwanni cikin sauri.

Masu aikin kai sakwanni na hada masu saye da sayarwa. Idan aka samu matsala daga wani bangare, to hakan kan kawo tsaiko ga masu kai sakwannin. Jiang kan yi kokarin kyautata mu’amala tsakaninta da ko wanne bangare. “Yana da kyau a rika kyautata mu’amala, tare da fahimtar juna. Kada ka yi kuskure saboda kana sauri. Na san mutanen da suke aiki a dakunan cin abinci dake kusa, saboda ina yawan hira da su idan ina da lokaci, kuma muna kulawa da junanmu idan bukata ta taso,” cewar Jiang.

A shekarar 2021, Jiang ta zama shugabar tawagar masu kai sakwanni a manhajar Meituan dake Shajing. A matsayin matashiya, tana ganin jagorantar maza babban nauyi ne. Amma ba da jimawa ba, suka fara girmama ta, saboda hazakarta. Tana aiki tukuru inda ya kasance tamkar tana kan hanya a ko da yaushe. Wani abokin aikinta ya ce, “Tuni take fara aiki tun muna barci. Idan muna hutawa ma, tana kan hanya.”

Jiang ta kan shirya taro game da aiki sau daya a kowanne mako, inda take gabatar da sabbin dabaru da ka’idoji, tare da tattaunawa game da matsalolin da suka auku a makon da ya gabata, kamar na rashin kai odan a kan lokaci da tsokaci rashin gamsuwa daga kwastomomi da rashin mu’amala mai kyau. Jiang wadda ta kasance jajirtacciya kuma mai nagarta, ta tabbatar da cewa ita shugaba ce ta kwarai.

Galibin mambobin tawagarta sun yi aiki da ita tsawon shekaru da dama. “Tana burge mu duk da kankantar shekarunta. Tana da kwarewa, kuma shugaba ce mai nagarta. Tana jagorantarmu yadda ya kamata,” cewar wani abokin aikinta. Sai dai Jiang, tana da tawali’u. Ta ce, “kowa yana min kirki saboda ni ce karama.”

Jiang kan yi amfani da lokacin da ba ta aiki wajen yin karatu, ta yadda za ta inganta basirarta. Misali, tana daukar darasin kwamfuta, haka kuma tana karanta littattafai masu alaka da tafiyar da harkokin gudanarwa. Tana fatan samun isassun kudaden fara kasuwancinta na kanta.

Aiki a matsayin mai jigilar kai abinci ya sauya rayuwar Jiang Xiaoxi. Cikin shekarar farko da farawa, Jiang ta biya bashin kudin magungunan mahaifiyarta da ake bin iyayenta. A shekara ta biyu, ta ginawa iyayenta gida a garinsu. Haka kuma ta hadu da masoyinta yayin da take aiki. Sun fara soyayya, sannan sun shirya yin aure a bana. Saurayinta ya ce, “abun da ya fi burge ni shi ne hazaka da dabi’unta. Ta kansace tamkar rana dake kawo haske da kuzari ga duk wandanda ke tare da ita.”

“Muddin za ka zama jajirtacce, to za ka samu sa’a. Birnin Shenzhen cike yake da kuruciyata. Ina fatan gina rayuwa mai kyau da cimma burina a wannan birnin mai cike da kuzari,” cewar Jiang Xiaoxi. (Kande Gao)