Haɗin Gwiwar Sin Da Majalisar Ɗinkin Duniya Na Da Tasiri Ga Makomar Zaman Lafiyar Duniya
2023-07-10 16:06:29 CMG Hausa
Ƙasar Sin a matsayinta na mamba a ƙungiyar ta duniya wato Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ba da shawararta na tabbatar da ra'ayin bangarori daban-daban na gaskiya, kuma tana son taƙaita rashin daidaiton tattalin arziki da zamantakewar al'umma da ke illa ga yankunan duniya. Inganta haɗin gwiwa tsakanin Sin da MDD wajen samun ci gaba mai ɗorewa, da sauyin yanayi, da kirkire-kirkire na zamani, da kare hakkin dan Adam, wani babban mataki ne na tabbatar da daidaito da dawwamar zaman lafiyar a duniya.
Ƙasar Sin na ci gaba da ciyar da wakilcin yankin kudu na duniya gaba ta hanyar faɗaɗa shirinta na BRICS da shirinta na shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya (BRI), tare da samar da kuɗaɗe masu sassaucin ƙa’idoji ga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, da ƙara ƙarfin muradun ci gaba mai ɗorewa (SDGs) a ƙasashen Afirka da dama.
Dangane da manufofin Majalisar Ɗinkin Duniya, BRI na ci gaba da tallafa wa ɗimbin ƙasashe masu tasowa a yunkurinsu na samun ci gaba mai ɗorewa, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ke kallonsa a matsayin wani muhimmin jagoranci kan ci gaban fasaha.
Tuni MDD ta yi gargadin cewa, alfanun irin wannan sauyi ya karkata sosai zuwa ga ƙasashe masu arziki, yana mai jaddada muhimmancin kiyaye ƙarin "abokan haɗin gwiwa" da ƙasar Sin, don taimakawa wajen cimma burin SDG.
A matsayinta na ƙasa mai tasowa mafi girma, Sin ta fahimci muhimmancin jagoranci kan kare hakkin dan Adam da daidaiton jinsi. A gun taron kwamitin kare hakkin bil adama na MDD karo na 53 da aka gudanar, ƙasar Sin ta yi na'am da kiraye-kirayen da ƙasashe kusan 80 suka yi na ƙarfafa haɗin kai, maimakon rarrabuwar kawuna, wajen tinkarar ƙalubalen hakkin dan Adam.
Hakazalika, ra'ayin Sin game da ’yancin ɗan adam ya samar da gagarumar nasara a kan yaƙi da matsananciyar talauci, musamman ga ƙasar da ta kai kusan kashi biyar na al'ummar duniya, bisa la'akari da irin wannan fa'ida, ƙasar Sin ta bude wani sabon salo na haɗin gwiwar raya ƙasa tare da MDD, wanda ya ƙunshi shigar da ’yan kasuwa sama da 650 na ƙasar Sin a cikin yarjejeniyar duniya ta MDD kan ’yancin dan Adam, da samar da ayyukan yi, da muhalli da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Yayin da ake fuskantar barazanar koma bayan tattalin arziki, da rashin tabbas na ci gaba, da rikice-rikice masu yawa, yana da matuƙar muhimmanci ga MDD da Sin su zurfafa alaƙa, da magance giɓin da ake samu wajen zaman lafiya, da ci gaba da shugabanci.
Shirin raya ƙasa da ƙasa (GDI) da ƙasar Sin ke jagoranta, shi ma wani kyakkyawan misali ne na ci gaban da aka samu tare. Majalisar Ɗinkin Duniya ta tallafa wa asusun haɗin gwiwar kudu-maso-kudu na GDI, albarkatun da ke baiwa ƙasashe damar shawo kan matsalolin kuɗi da kuma kawo cikas ga maƙasudan ci gaba mai ɗorewa.
A yayin da ɓangarorin biyu ke ƙoƙarin yin haɗin gwiwa kan ayyukan sauyin yanayi a duniya, goyon bayan da ƙasar Sin ta bayar na haɗin gwiwa a fannin makamashi mai tsafta a duniya, wata shaida ce ta yaƙi da rikice-rikicen da ake fuskanta.
Ƙarfafa haɗin gwiwa tare da Sin a fannoni daban-daban, ya sake jadadda wannan batu na cewa, “Haɗin gwiwar Sin da Majalisar Ɗinkin Duniya na da tasiri ga makomar zaman lafiyar duniya”. (Yahaya Babs)