logo

HAUSA

Bangare Japan da ya dage sai ya zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku zai sha kunya ta tsawon tarihi

2023-07-08 16:27:39 CMG Hausa

A ranar 7 ga wata, Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya ta Japan, ta ba da takardar shaidar amincewa da na’urorin zubar da dagwalon ruwan nukiliya na Fukushima, ga Kamfanin Wutar Lantarki na Tokyo. Hakan na nufin gwamnatin Japan ta kara daukar wani mataki na shirin zubar da dagwalon ruwan nukiliyar cikin teku, duk da tsananin adawa da hakan ke fuskanta a cikin gida da waje.

Kungiyoyin fararen hula da dama a jihar Fukushima, da sauran wuraren kasar sun sanar a wannan rana cewa, mutane 254,000, sun rattaba hannu kan adawa da wannan shirin. Wani binciken hadin gwiwa da kafafen yada labarai na Japan, da Koriya ta Kudu suka gudanar, ya nuna cewa, sama da kashi 80% na al'ummar Koriya ta Kudu, ba su amince da shirin na Japan ba.

Kaza lika jama’a a kasashen tsibiran tekun Pasifik, da Philippines, da Indonesia, da Afirka ta Kudu, da Peru, da sauran kasashe da dama, sun yi korafi game da wannan batu a ’yan kwanakin nan. Hakan na nuni da cewa, matakin da kasar Japan ta dauka na zubar da dagwalon ruwan nukiliya a cikin teku, wanda ya saba wa ra’ayin al’ummar duniya, bai samu amincewa ba.

Domin tsimin kudi, Japan tana daukar tekun Pasifik a matsayin magudanar ruwa, wanda hakan zai rataya mata diyyar kasashen duniya ta fuskokin da’a da sanin ya kamata.

Idan har Japan ta dage sai ta zubar da dagwalon ruwan nukiliyar ta cikin teku, to tabbas hakan zai sanya ta jin kunya ta tsawon tarihi.

(Mai fassara: Bilkisu Xin)