logo

HAUSA

Sin ta yi nasara kan kasar Japan a babbar gasar kwallon kwando ta Asiya

2023-07-06 21:00:18 CMG Hausa

Kungiyar kwallon kwando ajin mata ta kasar Sin, ta doke takwararta ta Japan da maki 73 da 71, a wasan karshe na lashe kofin Asiya da suka kara ranar Lahadin karshen makon jiya.

Da wannan nasara, Sin din ta karya tarihin rashin nasarar lashe kofin na tsawon shekaru 12 a jere. Rabon da Sin ta dauki wannan kofi tun shekarar 2011.

Bayan kammala wasan na karshe, babbar kocin kugiyar ta Sin Zheng Wei, ta shaidawa manema labarai cewa, tana jin wannan nasara tamkar almara, domin kuwa ita da sauran ‘yan wasan ta, ba su yi tsammanin daukar wannan kofi ba. Ta ce "Kafin fara gasar, lokacin da muke atisaye, muna da wasu matsaloli, kamar jinya da wasu ‘yan wasan mu ke fama da ita, kuma ba duk ‘yan wasan mu ne suke cikin tawagar tun daga farko ba. Sai dai daga lokacin da muke atisaye, zuwa lokacin da muke shirin fara buga wasanni a turai, kungiyar mu ta ci gaba da karfafa".

A nata bangare, kyaftin din kungiyar Li Meng, ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasancewar kungiyar ba ta samu damar daga wannan kofi cikin shekaru 12 da suka gabata ba, ‘yan wasan na Sin na ganin mawuyaci ne su iya samun damar lashe gasar ta wannan karo. Li ta ce "Mun aiwatar da dabarun da koci ta koyar da mu, don haka mun ji dadin wasan da muka buga".

Li ta kara da cewa, “Mun rika samun kwarewa sannu a hankali bayan duk wasa daya da muka buga a wasannin rukunoni", dukkanin ‘yan wasan mu sun hada kai da juna, mun yi musayar kwarewa, mun rika kallon bidiyon wasannin baya domin gano karfin mu da inda muka gaza. Yayin da gasar ke kaiwa ga wasannin karshe, mun riga mun gina kwarewar wasa tare, tsakanin dukkanin ‘yan wasan mu".