logo

HAUSA

Hadin gwiwa da kasar Sin na ingiza bunkasar kasashen Afirka

2023-07-06 17:10:48 CMG Hausa

Yayin da kasar Sin tare da kasashen Afirka ke kara azamar cika alkawuran da suka yiwa juna, na bunkasa hadin gwiwa da cudanya ta bangarori da dama, masharhanta na cewa “Kwalliya tana biyan kudin sabulu”, inda tuni hadin gwiwar kasar Sin da kasashen na Afirka ya haifar da ci gaban tattalin arziki, da kyautatuwar zamantakewar al’ummun sassan biyu. Alal misali, mun ga yadda bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 3 da ya gabata, ya kara karfafa alakar cinikayya, da tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da kara tabbatar da matsayin kasar Sin, na kasancewar muhimmiyar abokiyar cudanyar kasashen na Afirka a wannan fanni.

Idan ba a manta ba, yayin baje kolin na bana, wakilai daga kasashen Afirka 53, da karin wasu hukumomin kasa da kasa da dama sun hallara, kuma adadin masu baje hajoji a bikin ya kai 1,500, adadin da ya karu da kaso 70 bisa dari kan na shekarar 2021. Albarkacin matakai daban daban da sassan biyu ke dauka na raya huldar cinikayya da kasuwanci, yanzu haka Sin ta kai matsayin abokiyar cinikayyar Afirka mafi girma, kuma kasa ta hudu a girman zuba jari a nahiyar.

Bisa huldodin da Sin da kasashen Afirka ke rayawa, tasirin Sin a fannin bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka ya wuce batun samar da ababen more rayuwa kadai, domin kuma ya kunshi karin sassan samar da ci gaba daban daban. Ciki har da gina yankunan raya tattalin arziki na musamman da Sin din ke daukar nauyi a kasashen nahiyar da dama, wanda hakan ke samar da karin damammaki na bunkasa fannin masana’antun Afirka, da kuma kara fadada guraben ayyukan yi.

A daya bangaren, su ma kasashen Afirka ba a bar su a baya ba, wajen bullo da tsare-tsaren bunkasa cinikayya, da zuba jari tsakaninsu da bangaren Sin. Ga misali, yayin taron baje kolin kasa da kasa karo na 47 da ya gudana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzania a farkon makon nan, an kebe ranar Talata a matsayin ranar kasar Sin, tare da kebe rumfuna sama da 100 na baje hajojin kamfanonin kasar.

Wannan mataki dai ya kasance wata dama dake kara jaddada muhimmancin alakar cinikayya tsakanin Sin da Tanzania, da ma sauran kasashen Afirka, wadda a wannan karo ta baiwa masu yawon bude ido zarafin kara fahimtar wannan kasa mai ni’ima da karbar baki.

Manazarta da dama na ganin a halin da ake ciki, Sin da kasashen Afirka na kara fadada cudanya mai armashi ta fuskoki da dama, ta yadda hakan ke haifar da karin damammaki ga junan su, da habaka samar da ababen more rayuwar jama’a musamman a kasashen Afirka, da ingiza ci gaban masana’antu da musaya, matakin da ko shakka babu, na yin matukar tasiri ga ci gaban kasashen Afirka, a matsayin su na kasashe masu tasowa. (Saminu Alhassan)