logo

HAUSA

Bayan Kin Gaskiya…

2023-07-05 19:52:00 CMG Hausa

Da alamun dai Japan ba ta hakura da shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku ba, duk da kiraye-kiraye da sassan kasa da kasa ke mata kan illar da hakan ga rayuwar daukacin bil-Adama.

Wannan ne ma ya sa kasar Sin ta sake ankarar da Japan din, da ta yi la’akari da kimiya, ta kaucewa aukuwar hadari da ma yin komai ba tare da wata rufa-rufa ba game da shirin nata.

Kasar Sin da ragowar kasashen duniya, na fatan Japan za ta yi matukar la’akari da damuwar sassan kasa da kasa da ma al’ummarta a cikin guda. Wani abin takaici shi ne akwai rahotannin kafofin watsa labarai dake nuna cewa, Japan ta shawo hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya game da rahotonta na karshe, mai nasaba da tsarin Japan din na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, lamarin da ya kara sanya kasashen duniya cikin damuwa, domin rahoton hukumar ba ya nufin an amince Japan ta zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku. Wai yaro bar murna karenka ya kama zaki.

Ya kamata Japan ta fahimci cewa, zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, daidai yake da dawo da hadarin illar nukiliya ga daukacin bil-Adama, kuma wannan matakin da kasar Japan ta dauka, ya saba wa muradun da'a na kasa da kasa, da dokokin kasa da kasa kamar yarjejeniyar MDD kan dokar teku, da yarjejeniyar London ta hana gurbatar ruwa ta hanyar zubar da sharar gida da sauran al'amura.

Masharhanta dai na bayyana cewa, abu mafi fa’ida shi ne Japan, da ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku, maimakon haka ta sarrafa shi ta hanyar kimiyya, aminci da gaskiya, ta kuma hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, don aiwatar da matakan da suka dace game da tsarin sa ido na kasa da kasa na dogon lokaci, wanda zai shafi makwabtan Japan da sauran masu ruwa da tsaki ba tare da bata lokaci ba. Haka kuma ya wajaba hukumar IAEA ta gabatar da rahotonta na nazari bisa goyon bayan kimiya da tarihi, maimakon amincewa da matsayar Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku. Ya dace Japan ta fahimci cewa, bayan kin gaskiya fa, sai bata, kuma tsalla daya ake yi a fada rijiya, amma sai an yi dubu kafin a fito.

Don haka, Japan tana da sauran lokaci na gyara wannan batu, don gudun dan da na sani….(Ibrahim Yaya)