logo

HAUSA

Yadda kasashen Sin da Afirka ke kara hada-hadar cinikayya a tsakaninsu

2023-07-05 13:34:57 CMG Hausa

A ranar Lahadin karshen mako ne, aka kammala bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka karo na uku a birnin Changsha. A yayin bikin na wannan karo, bangarori daban daban sun sanya hannu a kan yarjejeniyoyi 120, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 10.3, kuma jimilar kudaden cinikayya da aka cimma a yayin baje kolin ta kai dala miliyan 400.

Bugu da kari yayin bikin an tsara ayyukan hadin gwiwa guda 99, wadanda darajar kudinsu ta kai dalar biliyan 8.7, kuma a cikin kasashen Afirka mahalarta, 11 sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa 74, adadin da ya haura wanda aka gudanar a bikin da ya gabaci. 

Kaza lika an fitar da sakamakon yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 34, kuma karo na farko ne aka fitar da ma'aunin cinikayyar Sin da Afirka, tare da kara fitar da rahoto kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya. 

Baje kolin wanda aka fara a shekarar 2019, ya kasance wani muhimmin dandali na inganta hadin gwiwar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Shekaru 14 ke nan a jere, kasar Sin tana zama babbar abokiyar kasuwanci a Afirka, bayan da ta doke Amurka a wannan fannin a shekarar 2009. Kawancen cinikayya da tattalin arzikin ba wai kawai ya zurfafa ba ne, har ma ya kara samun tagomashi tare da cin gajiya a tsakanin Sin da Afirka. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)