Fadin gonakin da aka girbe hatsi a lokacin zafi ya zarce hekta miliyan 20 a kasar Sin
2023-07-04 09:14:11 CMG Hausa
Masu kallonmu, barkanmu da war haka! Yanzu, an kusan kammala aikin girbin hatsi na lokacin zafi a duk fadin kasar Sin. Bayanai na nuna cewa, larduna tara, da suka hada da Henan, Anhui, Shandong, da Shanxi, sun girbe fiye da hekta miliyan 20 na alkama, kuma, an kusan kammala dukkanin ayyukan girbin alkama da injuna a manyan wuraren noman alkama a kasar Sin.