logo

HAUSA

Amfanin juna shi ne tushen hadin gwiwar Afirka da Sin

2023-07-03 15:39:54 CMG Hausa

Kowa na cewa yanayin tattalin arzikin duniya ba shi da kyau yanzu, amma idan ka halarci taron baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka, da ya gudana a birnin Changsha na kasar Sin a kwanakin baya, to, za ka ce kamar maganar ba ta yi daidai ba.

Saboda duk wani mutum da ya halarci taron ya ji mamakin yadda yanayin bikin ke da armashi, inda ake samun cunkuson mutane matuka. Alkaluman da aka gabatar bayan rufe taron baje kolin a jiya sun nuna cewa, cikin wa’adin taron na kwanaki 4, an nuna nau’ikan kayayyaki kimanin 1600 na wasu kasashe 29 dake nahiyar Afirka, inda aka samu mutane fiye da dubu 100 da suka halarci taron baje kolin, tare da kulla yarjeniyoyi 120, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 10.3.

Abun da ya fi burge ni a wajen taron baje kolin na wannan karo, shi ne yadda aka nuna dimbin kayayyakin amfanin gonan kasashen Afirka, irinsu kifaye na kasar Madagascar, da man zaitun na kasar Aljeriya, da tattasai na kasar Malawi, da dai sauransu. Kana wani nau’in ganyen shayi mai launin jar galura na kasar Kenya ya samu karbuwa sosai, saboda yadda yake kunshe da sinadarai masu gina jiki. Inda aka sayar da ganyen na ton 2, a cikin ranar farko da aka gudanar da bikin.

Ban da amfanin gona, an samu damar nuna wasu kayayyaki masu daraja kirar kasashen Afirka, irinsu tufafi, da lemu iri-iri, da kayan kwalliya na shafe-shafe, da dai sauransu, don neman shigar da su cikin kasuwannin kasar Sin. Cikinsu har da jakunkuna da tufafi masu kyan gani da wani saurayi dan kasar Zambia mai suna Kabaso ya kirkiro, wadanda suke da salon musamman na Afirka. A cewarsa, ya halarci taron baje kolin ne don yin bincike kan yanayin kasuwannin Sin, don neman sayar da kayayyakinsa ga karin jama’ar kasar.

Cikin abubuwan da aka nuna a wajen taron baje kolin, har da dandali na ciniki. Inda wani shafin yanar gizo mai taken Kilimall yake taimakawa sayar da kayayyakin Sin zuwa kasashen Afirka, gami da shigar da kayayyakin kirar kasashen Afirka cikin kasar Sin. Zuwa yanzu shafin nan ya sayar da kayayyaki na kimanin nau’ika miliyan 1 ga mutane fiye da miliyan 10, inda ta samar da guraben aikin yi fiye da 5000 a kasar Kenya kacal.

Sa’an nan ban da bikin baje koli, an gudanar da wasu bukukuwa kimanin 40 a gefen taron, tare da samar da sakamako mai gamsarwa. Misali, a wajen taron dandalin tattaunawar kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar kiwon lafiya da yin amfani da ganye wajen kare lafiyar jiki, bangarorin Sin da Afirka sun yi alkawarin daidaita ka’idojinsu na tantance ingancin kayayyaki a kwastam don magance yaduwar cutuka, ta yadda za a iya shigar da kayayyaki amfanin gonan kasashen Afirka cikin kasuwannin Sin cikin karin sauki. Kana a wajen wani taro na karfafa ciniki a fannin kayayyakin masana’antu, wani yankin masana’antu na lardin Hunan na kasar Sin ya kulla yarjejeniya tare da hukumar fitar da kayayyaki ta kasar Kodibwa, inda suka samar da shirin hadin gwiwa don raya masana’antu.

Sai dai, abin tambaya shi ne, me ya sa ake iya gudanar da bukukuwan masu alaka da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da ciniki cikin wani yanayi mai armashi, duk da wani yanayin tabarbarewa da tattalin arzikin duniya ke ciki? A ganina, zan iya yin amfani da maganar wani jami’in asusun Bill & Melinda Gates na kasar Amurka, mai suna Obai Khalifa, da ya fada wa ‘yan jarida a gefen taron baje koli na wannan karo, wajen amsa tambayar. A cewarsa, ya amince da yadda kasar Sin take kula da kasashen Afirka, inda ba ta kallon kasashen a matsayin nauyin da aka danka mata. Maimakon haka, kasar Sin ta dauki kasashen Afirka a matsayin abokan hulda, wadanda ake iya zuba musu jari don samun damar ci gaban tattalin arziki. Kana abubuwan da ya gani a wajen bikin baje kolin na wannan karo sun sa shi fahimtar huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, iri na amfanin juna.

Bayan da kayayyakin kasashen Afirka suka shiga cikin kasuwannin kasar Sin, masu samar da su dake kasashen Afirka za su samu karin kudin shiga, yayin da Sinawa za su samu damar more wadannan kayayyaki. Kana a lokacin da kamfanonin kasar Sin ke gudanar da wasu ayyuka a kasashen Afirka, lamarin zai ciyar da tattalin arzikin kasashen Afirka gaba, gami da haifarwa kamfanonin da riba. Dalilin yadda ake tsayawa kan manufar daidai-wa-daida da amfanin juna, ya sa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da ciniki ke dinga samun ci gaba, inda ake ba da gudummuwa ga kokarin kawar da wani yanayi na rashin tabbas a duniyarmu. (Bello Wang)