logo

HAUSA

Daidaiton Ƙasar Sin na taka muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Ƙasashen Duniya

2023-07-03 18:56:20 CMG Hausa

"Ya kamata a ƙara rungumar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yayin da duniya ta tsunduma cikin rikice-rikice da rashin zaman lafiya," waɗannan kalaman firaministan ƙasar Sin Li Qiang ne yayin da yake jawabi a wajen buɗe taron shekara-shekara na sabbin jagorori karo na 14, wanda aka fi sani da Davos na lokacin zafi, da ya gudana a ranakun 27 zuwa 29 na Yuni a Tianjin, ƙasar Sin.

Taron da ya samu mahalarta kusan 1,500 daga fannoni daban daban kama daga 'yan kasuwa, hukumomin gwamnatoci, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma malaman jami'o'I daga ƙasashen duniya kusan 100, kalaman Li saƙo ne zuwa ga al'ummar duniya da ke fuskantar rashin zaman lafiya da rikice-rikicen siyasa da bambance-bambancen aƙida suka haifar. Dunƙulewar kasuwancin duniya na fuskantar barazanar takunkumi na bai-ɗaya daga wasu ƙasashen yamma. Kana, yunƙurin samun haɗin gwiwar kimiyya ya samu cikas ta hanyar siyasa. Haka kuma yunƙurin yin musayar al'adu ya samu cikas ta rashin yarda, matsin lamba da rikice-rikicen siyasa.

An amince da ƙasar Sin a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi cin gajiyar dunƙulewar duniya. Wannan gaskiya ne, tun bayan da aka yi gyare-gyare da bude ƙofa ga waje, ƙasar Sin ta samu nasarorin da ba a taba ganin irinta ba a harkokin mulki. Ta kawar da matsanancin talauci ta hanyar fitar da mutane kusan miliyan 800 daga kangin talauci. A tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021, alkaluman bankin duniya sun nuna cewa, ƙasar Sin ta ba da gudummawar da ya kai kashi 38.6 cikin ɗari ga tattalin arzikin duniya. Haka kuma a lokacin da duniya ke cikin annobar COVID-19 da kuma bayan cutar, ƙasar Sin ta kasance jigon ci gaba mai ƙarfi yayin da sauran manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ke fafutukar samar da ingantaccen ci gaban GDP.

Tattalin arzikin ƙasar Sin yana da matuƙar fa'ida. A yayin da tattalin arzikin duniya yake ƙaruwa da kashi 2.8 cikin ɗari a shekarar 2023. "Tattalin arzikin Sin ta kai kusan ninki biyu, a ƙalla fiye da kashi 4 cikin ɗari. Don haka, har yanzu tattalin arzikin ƙasar Sin na samun bunƙasuwa cikin sauri fiye da yawancin tattalin arzikin ƙasashen duniya."    

Ci gaba da zurfafa kasancewar kamfanonin ƙetare a kasuwannin kasar Sin, da zuba jari, shi ma ya kasance kyakkyawan aminci da cikakken kwarin gwiwar da ƙasashen duniya ke da shi game da bunƙasuwar tattalin arzikin ƙasar Sin.

Mummunar fahimtar da wasu kafafen yaɗa labarai na yammacin Turai ke yi ma tattalin arzikin ƙasar Sin ba zai yi tasiri ga yunƙurin dunƙulewar duniya waje guda da gano hanyoyin samun ci gaba da farfadowar tattalin arziki ba.

Ƙasar Sin ta kasance wata muhimmiyar madogara ga ci gaban tattalin arzikin duniya a cikin shekaru goma da suka gabata. Ƙasashen duniya dole su yi haɗin gwiwa tare da keta hazo don ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.

Wannan dalili ne ya sanya yin adawa da ƙasar Sin tamkar ɓata lokaci ne. Kalmomi kamar “a guji” ko “a yi nesa” da ƙasar Sin sun zama sanannu a siyasar yammacin duniya, da aka yi amfani da su don ƙasashen yammacin duniya su ƙyamaci ƙasar Sin. Sai dai da’awarsu ba ta yi tasiri ba saboda ai “bindin raƙumi ya yi nesa da ƙasa”.  (Yahaya Babs)