logo

HAUSA

Kila yin barci kadan bayan karfe 10 na dare zai amfana wa lafiyar zuciya

2023-07-03 08:53:34 CMG Hausa

 

Masu nazari na kasar Birtaniya sun gano cewa, watakila yin barci tsakanin karfe 10 zuwa 11 na dare, zai fi amfanawa lafiyar zuciya. Wadanda suka yi barci na tsawon wannan lokaci, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon zuciya da shan inna ba ta da yawa gwargwadon sauran lokuta.

Masu nazarin daga jami’ar Exeter ta kasar Birtaniya sun samu sakamakon ne bayan da suka tantance bayanan da suka shafi masu aikin sa kai fiye da dubu 88 dangane da barcin da suke yi da ma lafiyar jikinsu, wadanda matsakaicin tsawon shekarunsu ya kai 61 da haihuwa.

Masu nazarin sun bukaci masu aikin sa kan su dauki kwanaki 7 a jere suna sanya agogon musamman wanda ke tattara bayanan barcinsu, a kuma binciko lafiyarsu da kuma amsa tambayoyi game da zaman rayuwarsu. Masu nazarin sun dauki shekaru 6 suna bibbiyar lafiyar masu aikin sa kan. Inda suka gano cewa, wasu fiye da dubu 3 sun kamu da cututtukan dake da nasaba da jijiyoyin zuciya.

Bayan da masu nazarin suka yi nazari kan wadannan masu aikin sa kai, sun gano cewa, yin barci tsakanin karfe 10 zuwa 11 na dare, ya fi dacewa da mutane. Wadanda suka yi barci kafin karfe 10 na dare, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cutar jijiyoyin zuciya ta karu da kashi 24 cikin kashi dari, kana wadanda suka yi barci tsakanin karfe 11 zuwa 12 na dare, barazanar ta karu da kashi 12 cikin kashi dari. Sa’an nan kuma wadanda suka yi barci bayan karfe 12 na dare, barazanar ta karu da kashi 25 cikin kashi dari. Duk da la’akari da tsawon lokacin barci da kuma sauya lokacin barci a kullum, masu nazarin sun gano cewa, akwai alaka tsakanin lokacin yin barci da kuma barazanar kamuwa da ciwon zuciya.

Masu nazarin sun yi karin haske da cewa, ko da yake ba a tabbatar da cewa, lokacin yin barci, na daga cikin dalilan kamuwa da ciwon zuciya ba. Amma yin barci kafin karfe 10 na dare ko kuma bayan karfe 11 na dare, zai yiwu yana rikitar da tsarin yanayin jiki, ta haka za a illanta lafiyar jijiyoyin zuciya.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, yin barci bayan karfe 12 na dare, zai fi illanta lafiyar jijiyoyin zuciya, saboda hakan ya kan sa a tashi daga barci a makare kashegari, a kuma rasa damar jin dadin hasken rana na safe, wanda yake taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin yanayin jiki. (Tasallah Yuan)