logo

HAUSA

“Saukakawa", "gudu", "kwazo"... Mahimman kalmomi na Sin a idanun Jinjin, 'yar Kyrgyzstan

2023-07-03 20:54:35 CMG Hausa

Jin Jin, 'yar Kyrgyzstan ce, wadda ta shafe fiye da shekaru hudu tana zaune a kasar Sin, inda take matukar sha'awar yadda Sinawa ke yin aiki tukuru da kuma yin nazari sosai kan karatu, lamarin da ya sa ta kara sha'awar wannan kasa. A cikin shirinmu na yau, za mu hadu da wannan baiwar Allah mai suna Jin Jin dake zaune da kuma karatu a birnin Xi'an dake arewa maso yammacin kasar Sin.

“Ina so in je birnin Shanghai, ina so in je birnin Beijing, ina kuma so in je birnin Harbin, ina son in ci hotpot na lardin Sichuan, ina so in je birnin Guangzhou, ina son tafiya...”

Mai maganar ita ce Jin Jin, ‘yar Kyrgyzstan, kuma daliba ce dake aji na uku a Jami'ar Arewa maso Yamma ta kasar Sin.

Ana fassara ainihin sunan ta a matsayin "watan zinare" a cikin harshen Rashanci, don haka ta ba wa kanta suna mai kyau na Sinanci - "Jin Jin", wanda kuma ke nufin zinariya. Ko da yake ta shafe fiye da shekaru hudu tana zaune a kasar Sin, amma sha'awar ta kan wannan "kasa mai ban mamaki" da ke fitowa a cikin littattafan karatun sakandare a wurinta bai ragu ko kadan ba, har ma tana karuwa.

"A lokacin da nake makarantar sakandare, mun yi nazarin tarihi, malamin tarihi ya ce, akwai abubuwan al'ajabi guda bakwai a duniya, na farko ita ce babbar ganuwa da ke birnin Beijing. Na yi tunani a raina cewa, babbar ganuwa tana da tsayi sosai, da alama akwai sihiri. A kasashen waje, ina yawan kallon fina-finan Jackie Chan, kuma ina tsammanin kowane dan kasar Sin na iya wasan Tai Chi da Kung Fu.”

A wancan lokacin, yaya ta wacce ta girme ni da shekaru 9, ta zabi yin karatun Sinanci a jami'a, inda ta shuka iri na karatu a kasar Sin a cikin zuciyar Jin Jin. Lokacin da ta iso kasar Sin a zahiri, Jin Jin ta gano cewa, ban da kasancewarsa "littafin tarihi marar iyaka", zamanantar da Sin da saurin bunkasar da kasar, su ma sun kasance mai ban sha'awa. A zaman rayuwar Jin Jin, ana iya ganin alamar "gudun Sinanci" a ko'ina.

"Misali, ana isar da sako cikin sauri sosai a nan kasar Sin, a wasu sauran kasashe sai an jira kusan mako biyu ko mako daya, amma bayan na zo kasar Sin sai sako ya zo cikin kwana biyu kawai. Baya ga haka, a kusa da makarantarmu, an gina wani sabon gini a cikin watanni uku. Na yi tunani a raina, shin wannan gaskiya ne? ta ya aka yi, ya yi sauri haka! ?”

Jin Jin ta ce, Sinawa suna aiki da yin karatu tukuru a salon rayuwa mai sauri, suna mai da hankali kan sana'o'insu da karatunsu, suna kuma mai da hankali kan ci gaban kansu, abin da ta yaba sosai.

“A lokacin da nake karatu, na dauki darasi tare da abokan karatuna na Sinawa, sun kasance masu himma da kwazo wajen karatunsu, kuma suna takura wa kansu. Suka ce, 'Idan an yi jarrabawa, akwai sabbin kalmomi 100 a cikin jarrabawar, dole ne mu tuna da sababbin kalmomin 1000'. Gaskiya wannan ya burge ni sosai.”

Ya zuwa yanzu, Jin Jin ta riga ta shafe shekaru fiye da uku tana zaune a birnin Xi'an. Daga Mutum-mutumin soja na daular Qin zuwa Husumiyar Dayan, daga Hasumiyar buga kararrawa zuwa Titin ‘yan kabilar Hui ... Lokacin da take magana game da shahararrun wuraren al'adu a Xi'an, ta san komai game da su. Tana son sanya kayan gargajiya na kasar Sin, kuma tana yawo a cikin gine-ginen gargajiyar kasar, tana kuma son yawo kan tituna da lungu-lungu, don neman kayan abinci masu dadi dake da halin musamman na wurin.

Jin Jin ta ce, Xi'an ba wai babban birnin kasar Sin na tsawon shekaru dubu ba ne da ke da dimbin al'adun gargajiya kadai ba, wani birni ne na zamani mai bude kofa ga kasashen duniya. Jin Jin ta ga 'yan kasashen waje da yawa suna zaune da kuma kasuwanci a birnin Xi'an, kuma Xi'an ya yi maraba da su cikin farin ciki da gaskiya. Wannan ya sa Jin Jin ta kara daukar wannan wuri a matsayin "gidanta" na biyu.

“A cikin shekara ta farko da na zo kasar Sin, na yi rashin gida kuma ina so in koma kasata. A cikin shekara ta biyu, sannu a hankali na saba da rayuwa a kasar Sin, mun fita wasa sannan muka tattauna da abokan karatuna na Sinawa. A gani na suna da matukar ban sha'awa da saukin yin abota…A shekara ta uku, na daina jin kadaici a kasar Sin, a shekara ta hudu, ba na son komawa gida.”

A shekarar da ta gabata aka cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Kyrgyzstan da Sin, Jin Jin ta ce, a cikin 'yan shekarun nan, ana ta karfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu, wanda ya kara samar da damammaki na samun bunkasuwa ga kasashen biyu. Jin Jin tana shirin ci gaba da karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci na kasa da kasa bayan kammala karatun digiri na farko, kuma a ganinta ya kamata a yi fatan samun aikin yi a nan gaba.

“A cikin 'yan shekarun nan, koyon Sinanci ya samu karbuwa sosai a kasarmu, a kan zabi yin karatu a kasar Sin, sannan a koma kasarmu don taimakawa mata wajen samun bunkasuwa. Ban da haka, akwai kamfanonin kasar Sin da yawa a Kyrgyzstan, saboda haka, ina iya zaben yin aiki a can bayan na kammala koyon Sinanci. Ina so in koyi kasuwancin kasa da kasa, ta yadda zan iya gabatar da wasu kayayyaki masu kyau daga kasar Sin zuwa Kyrgyzstan, haka kuma zan iya kawo kayayyakin Kyrgyzstan zuwa kasar Sin.”