logo

HAUSA

Me ya sa Amurka ta sake komawa UNESCO bayan da ta sha ficewa daga hukumar?

2023-07-02 21:28:28 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

 

Amurka za ta sake komawa hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adu ta MDD, wato UNESCO a takaice.

A ranar 30 ga watan Yuni, an zartas da wani daftarin kuduri yayin taron musamman na babban taron UNESCO, inda aka amince da maido da kujerar kasar Amurka a hukumar tun daga watan Yulin da ake ciki daga dukkanin fannoni. Hakan nan ya zama karo na uku da Amurka za ta kasance mamban hukumar, wato bayan da ta fice daga hukumar a shekarar 1984 da ta 2018.

Amma me ya sa Amurka ta sake komawa hukumar? Me ya sa kuma ta sha komawa bayan ficewa?

Wata kila muna iya gano amsar tambayar daga jawabin da mataimakin sakataren harkokin wajen kasar John Bass ya yi, a gun taron manema labarai da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta gudanar a watan Maris da ya gabata, inda ya ce, a ganin gwamnatin kasar Amurka, komawa hukumar UNESCO zai taimakawa Amurka wajen takarar da take yi da kasar Sin a duniya.

A hakika, a cikin ’yan shekarun baya, Amurka ta sha ficewa da kuma komawa hukumomi, da yarjejeniyoyi na kasa da kasa. Idan ba a manta ba, baya ga UNESCO, Amurka ta kuma fice daga yarjejeniyar Paris, da yarjejeniyar bakin haure ta duniya, da yarjejeniyar nukiliya ta Iran, da majalisar hakkin dan Adam ta MDD, da hukumar lafiya ta duniya da dai sauransu.

In dai mun yi nazari a kan dalilin ficewarta da komarta kuma, za mu gano cewa, kullum tana neman kujera a kungiyoyin duniya ne don biyan bukatunta, amma idan ba ta cimma buri ba sai ta fice. Lallai, don cimma moriyarta, da ma kiyaye babakeren da ta kafa ne take shiga kungiyoyin duniya.

Sai dai kuma neman wakilci a kungiyoyin duniya ba wasa ba ne, kuma bai kamata a mai da shi a matsayin dabarar yin takara da wasu don cimma burin siyasa ba.

Idan dai da sahihiyar zuci ne Amurka ke son komawa a wannan karo, to, ya kamata ta sauke nauyin da ke wuyanta, ta biya kudin karo-karo na hukumar yadda ya kamata, sa’an nan ta kiyaye cudanyar da ke tsakanin bangarori daban daban, da ma ikon mulki, da tsarinsu na mabanbantan kasashe, ta yi kokarin inganta fahimtar juna, da hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobin hukumar, don tinkarar kalubale na bai daya da duniyarmu ke fuskanta. (Mai Zane: Mustapha Bulama)