logo

HAUSA

Hannu daya ba ya daukar jinka——Sin da Afirka za su kara cimma nasarorin yaki da kwararowar hamada in sun hada kansu

2023-07-03 17:38:56 CRI

Watan Yuni da muke ciki wata ne da ke shafar kiyaye muhalli, kasancewar ana samun ranar kare muhallin duniya da ma ranar yaki da kwararowar hamada da fari ta duniya, duk a wannan wata, wadanda suke jan hankalinmu game da muhimmancin zaman jituwar ‘yan Adam da muhallinsu.

A nan kasar Sin, manufar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba na kara zame wa‘yan kasar jini da tsoka a rayuwarsu ta yau da kullum. Tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta fara gudanar da wani babban aikin dasa bishiyoyi a fadin kasar, kuma kawo yanzu fadin dazuzzukan da aka dasa a wannan aiki ya kai eka miliyan 68, matakin da ya sa kason dazuzzukan a fadin kasar ya karu zuwa kashi 24.2%, kuma fadin dazuzzukan da aka dasa ma ya zo na farko a duniya, an kuma cimma gagaruman nasarori a fannin yaki da kwararowar hamada. Musamman ma dazuzzukan da aka dasa a sassan arewaci da arewa maso yammaci da ma arewa maso gabashin kasar, wadanda ake yi musu kirarin “babbar ganuwa mai launin kore”, sun taka muhimmiyar rawa ta fannonin kiyaye muhalli da bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma.

Nasarorin da aka cimma ta fannin inganta muhallin zama ba alkaluma ba ne ga al’ummar wannan kasa, kyautatuwar muhallin zama ne da suke gani da ido. Misali a birnin Beijing da nake rayuwa, a cikin ‘yan shekarun baya, dazuzzukan da aka dasa musamman domin mazauna birnin su shakata ko motsa jiki sun yi ta karuwa, kuma iska ma na kara inganta…kuma duk wadannan sauye-sauyen da ke faruwa ga rayuwata suna faranta mini rai sosai, amma abin da ya fi sa ni farin ciki shi ne yadda kasar Sin ke kokarin raba ingantattun fasahohinta ta fannin kyautata muhalli ga aminanta na Afirka, kasancewar a kwanakin nan na samu damar halartar kwas din samar da fasahohi wajen shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall (PAGGW), wanda aka  shirya a jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda na gane ma idona yadda masana da suka zo daga kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, ciki har da na Nijeriya da Nijer da Mauritania da Habasha da sauransu suka hadu da takwarorinsu na kasar Sin, don su gano bakin zaren warware matsalar kwararowar hamada.

Kwararowar hamada babbar matsalar muhalli ce da ke barazana ga rayuwar dan Adam da ma bunkasuwarsu, kuma da kasar Sin da nahiyar Afirka dukkansu na daga cikin yankunan duniya da matsalar ta fi addaba. Taklimakan, hamada ce mafi girma a kasar Sin, wadda take jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma ma’anar Taklimakan shi ne “in ka shiga, ba lallai ne ka fita ba”, a sakamakon irin mummunan yanayin da ke wajen. To, sai dai duk da irin wannan hali, an gina wata hanya mai tsawon kilomita sama da 520 da ta ratsa hamadar, kuma domin kare hanyar daga kwararowar hamada, kana a gefunan hanyar, an dasa dazuzzuka masu fadin sama da mita 70, wadanda tsayinsu ya kai kilomita sama da 430.

Mista Innocent Alenyi da ya halarci kwas din, wanda shi ne mataimakin darektan hukumar kula da aikin PAGGW a tarayyar Nijeriya, bayan da ya kai ziyara wannan hanyar da ta ratsa hamadar Taklimakan tare da gane ma idonsa dazuzzukan da aka dasa a gafunan hanyar, ya fada min cewa,“Abin da ya fi burge ni shi ne yadda suke samar da ruwa ga wadannan bishiyoyin, inda na ga sun haka rijiyoyi fiye da dari a dab da hanyoyin mota, don samar da ruwa ga dashen tsare rairayi. Wannan hanya, tsawonta ya kai fiye da kilomita 500, kana dimbin bishoyoyin da aka dasa don kare hanyar tsawonsu ma ya wuce kilomita 430. Gaskiya abun da na gani ya ba ni mamaki. Kuma muna son yin amfani da wadannan fasahohi wajen dakile kwararar hamada a Najeriya.”

Umar Danladi Dahiru, wanda shi ne darektan cibiyar dake rajin kare kwararowar hamada a kasashen Afirka (Africa Desertification Control Initiative Nigeria), shi ma yana daga cikin masu halartar kwas din, a yayin da yake ziyara a hamadar Taklimakan, wani gwajin da ake yi ya ba shi sha’awa matuka, kuma ya ce, “Wata sabuwar dabara da aka fito da ita ta yin wani gidan dara, wanda ake amfani da rogo, wanda yake shi kansa sabuwar dabara ce da masana suka fito da ita a nan kasar Sin, kuma tana kan gwaji a halin yanzu, amma ga dukkan alamu, sakamakon farko farko da ya fara fitowa a kan gwaji, wannan dabara zai yi amfani kwarai da gaske, maimakon a yi amfani da kirare ko kuma ciyayi na shinkafa, kuma yashin da zai tare ya fi yashin da wancan tsohuwar dabara take tarewa, wanda ya ba ni sha’awa kwarai da gaske.”

Yanzu fasahohin zamani na kara taka muhimmiyar rawa a fannin dakile yaduwar hamada. A kasar Sin, an kafa cibiyar nazarin bayanan da aka tattara ta yanar gizo ta Internet don taimakawa samun ci gaba mai dorewa a shekarar 2021. Wannan cibiya ita ma tana samar da taimako ga kasashen Afirka. Li Xiaosong, wani mai nazarin kimiyya da fasaha ne dake aiki a cibiyar, shi ma ya bayyana yadda kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa da kungiyar PAGGW, don yin amfani da fasahohin zamani ta fannin kyautata ingancin aikin yaki da kwararowar hamada, ya ce, “Aikinmu shi ne sa ido kan sakamakon da aka samu. Misali, a baya ba mu san ainihin sakamakon wasu ayyukan da muke yi ba, kuma ba a san ko ya kamata a ci gaba da gudanar da su ba. Saboda haka, yanzu muna yin amfani da taurarin dan Adam wajen gudanar da ayyukan sa ido a kai a kai, don duba ko matakan da aka dauka sun dace, kuma ko ana bukatar gyara dabarun.”

A tsawon kwanaki sama da 10 da ake gudanar da wannan kwas, irin musayar ra’ayoyi da fasahohi a tsakanin sassan biyu ba sa lissaftuwa. Burin bai daya na kyautata muhallin zama ya kusantar da kasar Sin da kasashen Afirka da juna da ma karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

A gun taron ministoci karo na takwas na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da aka gudanar a shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, inda ya jaddada goyon baya ga aikin shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall (PAGGW), kuma a game da wannan, mista Lei Jiaqiang, manazarci a cibiyar nazarin muhalli da bayanan kasa ta jihar Xinjiang ya ce,“yanzu haka muna kokarin aiwatar da wani shiri, wato mu tsara ‘shirin kasar Sin na goyon bayan PAGGW’ tare da gina lambun nuna fasahohin kare muhalli na tsakanin Sin da Afirka, ta hakan mu raba ingantattun fasahohin kasar Sin ta fannin kare kwararowar hamada, don taimakawa kasashen Afirka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma, ta yadda za mu tabbatar da kiran da shugaba Xi Jinping ya yi na goyon baya ga aikin shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall”.

Hannu daya ba ya daukar jinka, Marcelin Sanou, wani babban jami’i a sakatariyar kungiyar PAGGW, da wannan jimla ne ya bayyana hadin gwiwar Sin da Afirka ta fannin yaki da kwararowar hamada. Shi ma mista Endrias Geta Beldeda, mataimakin ministan kula da ban ruwa da shimfidaddun yankuna mara tudu na kasar Habasha, yana ganin cewa, ta fannin yaki da kwararowar hamada, shawarar shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall na daga cikin muhimman fannoni da sassan biyu ke iya yin kokari tare. Ya ce,“Kasancewar kasashen Afirka da kasar Sin suna da kyakkyawar hulda ta fannonin diplomasiyya da tattalin arziki da al’adu, wadda ake iya yin amfani da ita wajen tabbatar da kyakkyawar makomar bai daya gare su.”

Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, kullum makomarsu daya ce. Ta fannin yaki da kwararowar hamada, tabbas za su kara cimma gaggaruman nasarori in sun hada gwiwa da juna.(Lubabatu Lei)