logo

HAUSA

Wasannin gasar Olympics ta musamman ta samar da damar shigar kowa da kowa harkar motsa jiki in ji yar wasar Jamus

2023-06-29 21:31:35 CRI

 

Stefanie Wiegel matashiya ce mai shekaru 31 a duniya, wadda ke da bukata ta musamman, tana kuma cikin ‘yan wasan motsa jiki 7,000 da suka shiga gasar Olympics ta musamman ta 2023, wadda ta gudana a birnin Berlin na kasar Jamus tsakanin ranaikun 17 zuwa 25 ga watan Yunin nan.

Stefanie Wiegel, ta shiga rayuwar wasannin motsa jiki sosai, wanda hakan ya ba ta nishadi matuka. A cewar matashiyar “Na samu damar haduwa da mutane da dama, ina jin karsashi, na kuma more rayuwa sosai saboda wasanni”. A yanzu haka Wiegel, tana shiga wasannin takalmin taya, da allon zamiyar kankara.

Ta ce "Na samu karramawa da yabo masu yawa. Atisaye da gasanni, dama ce ta kawar da rabuwar kawuna tsakanin al’ummu". Yayin da take tsakiyar lashe lambobin yabo daban daban cikin shekaru masu yawa, tana samun farin ciki mai yawa, hakan wata dama ce ta sauya rayuwar ta baki daya. Daga baya a shekarar 2017, matashiyar ta zama kakakin ‘yan wasan motsa jiki su 14 ‘yan kasar Jamus.

Wannan dama da Wiegel ta samu ta jagorancin tawagar Jamus ta daga darajar ta, kaza lika hakan ya ba ta damar samun cin gashin kai a rayuwa. Kafin hakan, Wiegel na aiki ne a wani wurin kwadago dake jihar North Rhine-Westphalia, dake tsaanin birnin Duesseldorf da Leverkusen.

Sakamakon ci gaba, da goyon bayan da ta samu daga iyaye da iyalan ta, abubuwan da take yi na ayyukan yau da kullum sun daidaita mata rayuwa, tare da ba ta damar shawo kan kalubalen da take fuskanta.

A cewar mahaifin ta Dietmar Wiegel "Har kullum ina mamakin yadda ta samu ci gaba, da yadda ta zama mai iya dogaro da kan ta". Mista Dietmar dai yana halartar dukkanin atisaye da ‘yar sa ke gudanarwa, da ma dukkanin gasannin da ta fafata yayin gasar ta Berlin, inda ya kasance mai tallafa mata wajen cimma manyan nasarori.

Da take bayyana yadda take ji a ran ta, game da shiga gasannin lokacin zafi da na hunturu, Stefanie ta ce "In ba domin wadannan wasanni ba, da sai dai na zauna kawai a gida bana komai. Ina son haduwa da mutane daban daban, mu rika tattaunawa, tare da cimma nasarori. Ba tare da la’akari da sakamakon gasanni ba, har kullum ina jin dadin shiga cikin jama’a".

A ganin Wiegel, samun nasarar lashe lambar yabo ta gasar Olympic karin farin ciki ne dake biyo bayan cudanya da al’umma. Ta kuma bayyana yadda ta yi farin ciki da kasancewar kasar ta mai masaukin bakin gasar ta wannan karo, tana mai fatan ganin karin ci gaba a fannin raya wasannin dake iya hade dukkanin rukunonin al’umma baki daya.

Ta ce “Wannan dama da na samu, ta yin wasa a gaban iyali da abokai na, tare da haduwa da sauran ‘yan wasan motsa jiki daga kasashe da yankunan duniya kusan 190 abun farin ciki ne matuka”.

Yayin wannan gasar Olympics ta musamman ta 2023 da birnin Berlin ya karbi bakunci, an gudanar da nau’o’in wasanni 26, gasar ta kuma hallara ‘yan kallo sama da 300,000. Ita ce kuma mafi yawan nau’o’in wasanni na musamman da kasar Jamus ta karbi bakunci, tun bayan Olympic din birnin Munich, wadda ta gudana a shekarar 1972.

Gasar ta wannan karo ta kuma kunshi wasannin gargajiya, karkashin taken "Hadakar wasanni", kana ta fayyace burin hade damar shiga wasanni tsakanin dukkanin masu sha’awar motsa jiki, ciki har da rukunin jama’a masu bukata ta musamman.

A cewar Wiegel "Mun ji dadin wannan gasa, mun kuma dauke ta a matsayin ta kowa da kowa. Yana da muhimmanci mu rika shiga wasanni tare"……..

 

Special Olympic athlete Wiegel running life with help of inclusive sports

BERLIN, June 18 (Xinhua) -- Stefanie Wiegel is among the 7,000 athletes with disabilities vying for medals at the 2023 Special Olympics in Berlin.

Listening to the 31-year-old, one enters a world filled with the passion of a committed sportsperson. "It gives me so much. I meet people, I am active, and I enjoy life much more than without it," said Wiegel, an inline skater and snowboarder.

She emphasized that sports provides a platform for athletes to "receive appreciation and recognition." Training and competition, she added, seem to construct a bridge to what's perceived as a typical life.

While winning several medals over the years brings joy, it's the transformative power of sports that's made the most significant impact on Wiegel's life. She naturally stepped into the role of spokesperson for the 14 German athletes in 2017.

Assuming responsibility for the German team enhances her life, Wiegel said, alongside maintaining a certain level of independence in her daily life.

Wiegel works in a sheltered workshop in the federal state of North Rhine-Westphalia, nestled between Duesseldorf and Leverkusen.

With continuous support from her parents and family, a structured daily routine provides the stability she needs to navigate everyday challenges.

"I am always amazed at how she developed and how much independence she gained," said Dietmar Wiegel, Stefanie's father.

While he attends all of her training sessions and maintains close contact throughout the Berlin Games, he sees himself as a supporting figure in the background.

Stefanie's participation in both the Summer and Winter Games narrates her fervor for sports.

"Otherwise, I would only be sitting around at home, bored. I love to see other people, converse, and strive for goals. Regardless of the competition's outcome, I just love to be around," she explained.

To Wiegel, becoming an Olympic champion or winning medals seems to be a delightful byproduct of her participation.

The German athlete is thrilled about the Games taking place in her home country and hopes for further development in inclusive sports.

Competing at home in front of her family and friends and meeting athletes from 190 countries and regions is a phenomenal experience for her, she confessed.

The competitions in 26 disciplines are projected to draw the attention of over 300,000 spectators throughout the German capital.

The 2023 Games, running until June 25, represents the largest multi-sport event in Germany since the 1972 Olympic Games held in Munich.

Alongside traditional competitions, 16 events under the guideline "Unified Sports" will occur, demonstrating the value of inclusive sports where athletes with and without disabilities compete together.

"We enjoy it and take it as a normal thing. It's important we do sports together," Wiegel concluded.