logo

HAUSA

Rawar Taron Davos Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya

2023-06-28 10:28:48 CMG Hausa

Taron Davos taro ne da ake tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya. Taron bana dake zama na 14, zai gudana a birnin Tianjin na kasar Sin daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Yunin shekarar 2023.

A bana ana sa ran taron zai hallara mahalarta kimanin 1,500 daga bangaren gwamnati, da ’yan kasuwa da hukumomin kasa da kasa. Taken taron na bana shi ne karfin dake tafiyar da tattalin arzikin duniya, inda za a mayar da hankali kan wasu muhimman sassa guda shida da suka hada da sake fasalta hanyoyin samun bunkasuwa, da matsayin kasar Sin a harkokin kasa da kasa, batun makamashi, masu sayen kayayyaki bayan annobar COVID-19, kiyaye muhalli da matsalar sauyin yanayi, da kuma yadda za a ci gajiyar kirkire-kirkire.

A jawabinsa na bude taron, firaministan kasar Sin Li Qiang ya tabo batun hadin kai da goyon bayan juna, illar da annobar Covid-19 ta haddasawa duniya, matsalar sauyin yanayi, bashin dake wuyan kasashe, ci gaban duniya dake fuskantar tafiyar hawainiya, gibin ci gaba tsakanin kasashe da ma jama’a.

Haka kuma ana sa ran tattauna shirin raya duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar yayin babban taron MDD na 26 da ya gudana a watan Satumbar shekarar 2021. Masu sharhi na fatan taron na bana, zai fito da matakan da za su kai ga magance kalubalen da duniya ke fuskanta. (Yahaya, Ibrahim/ Sanusi Chen)