logo

HAUSA

Hada Kai Ba Hada Baki Ba Ne…

2023-06-28 17:39:58 CMG HAUSA

DAGA IBRAHIM YAYA

A makon da ya gabata ne, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya kammala ziyarar da ya kai kasashen Jamus, da Faransa, ziyarar dake da babbar ma’ana ga bangarorin biyu. A yayin wannan ziyara mai muhimmanci a wannan lokaci da duniya ke fama da rashin tabbas, jami’in na kasar Sin ya gana da wakilan kasashen biyu a fannin siyasa, da masana’antu, da kasuwanci, inda ya jadadda yadda bunkasuwar kasar Sin ta kawowa duniya damammaki maimakon hadari.

A duk inda Li Qiang ya ziyarta, ya kan jaddada matsayin kasarsa na mutunta juna da samun nasarar moriyar juna da hada kai don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma wadata a fadin duniya.

Su ma shugabannin kasashen biyu sun bayyana matsayin da suke kai na nuna adawa da ra’ayin katse huldar bangarorin biyu, da ma yaki da ko wane irin mataki na jayayya da juna, ko mayar da wani bangare saniyar ware. Sun kuma bayyana cewa, Sin da Turai na da matsaya daya game da kin katse huldarsu, da ingiza hadin kai, da samarwa duniya tabbaci bisa hali mai sarkakiya da duniyar ke ciki.  Wannan ya kara nuna cewa, ra’ayin bangarorin ya zo daya, matakin dake nuna cewa, duk mai neman illata wannan alaka ba zai taba yin nasara ba.

Idan ba a manta ba, tun daga karshen shekarar da ta gabata ce, shugabannin Sin da Turai ke kara yaukaka mu’ammala, da tuntubar juna, inda shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da sauran shugabannin kasashen Turai, suka ziyarci kasar Sin, tare da cimma matsaya daya bi da bi da shugaban Sin, kan yadda za su zurfafa dangantaka da hadin kansu.

Ziyarar Li Qiang ta wannan karo a Turai, na da zummar tabbatar da matsaya daya da aka cimma, da ingiza hadin kansu a fannoni daban daban. Ai dama hadin kai ba wai hada baki ba ne. Kuma da abokin daka ake shan gari. (Ibrahim Yaya)