logo

HAUSA

Noma Tushen Arziki

2023-06-27 20:01:39 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

Matsalar sauyin yanayi abu ne da a ko da yaushe ake ci gaba da tattaunawa kansa a duniya, domin lalubo bakin zaren warware mummunan tasirinta. A ci gaba da hakan ne, masana kimiyya na kasar Sin da na kasashen Afrika suka kira da a samo tsare-tsaren samar da abinci masu jure yanayi don kawar da yunwa a Afrika.

Kaso 2 zuwa 3 na hayaki mai guba da ake fitarwa a duniya ne kadai nahiyar Afrika ke fitarwa, amma ita ce ta fi dandan kudarta sabili da matsalar.  

Yayin da ake ja-in-ja da manyan kasashe kan cika alkawarin da suka dauka na tallafawa kasashe masu tasowa musammam na Afrika wajen shawo kan matsalar yanayi, kasar Sin, wadda ita ma kasa ce mai tasowa, na ci gaba da bada gudunmuwarta ta duk wata kafa da ta san zai haifar da alfanu.

Yayin wani taron tattaunawa da aka yi a Nairobin Kenya a jiya, masana Sin da takwarorinsu na Afrika, sun jaddada kiran bunkasa tsare-tsaren noma masu dacewa da yanayi da kuma juriya, domin shawo kan matsalar yunwa.

Ba mutum abinci tallafi ne mai kyau, amma samar masa yadda zai samu abincin da kansa, ya fi kyautuwa. Don haka Sin bata tsaya ga tallafawa kasashen Afrika mabukata da abinci da kudi da ma kayayyaki ba, tana ci gaba da hobbasa wajen ganin sun samu hanyar samarwa kansu abinci da kansu, domin ba wannan ne karo na farko da masanan Sin ke zuwa nahiyar Afrika domin koyar da dabarun nom ana zamani ba.

Yunkurin masanan na lalubo hanyoyin inganta noma kamar a ko da yaushe,  zai taimakwa gaya wajen shawo kan tarin matsalolin da ake fuskanta. Zai karawa manoma kwarin gwiwar dagewa wajen habaka aikin noma domin ciyar da al’umma wanda zai samar musu da karin kudin shiga da samar da karin guraben ayyukan yi.

Inganta tsare-tsaren noma za su taimaka gaya wajen kara jan hankalin matasa shiga harkar noma, lamarin da zai rage musu zaman kasha wando, da aikata muggan ayyuka tare da habaka tattallin arzikin kasashe. Idan muka yi nazari, wannan yunkuri idan ya tabbata, na iya shawo kan kusan dukkan matsalolin da nahiyar ke fuskanta, kamar yadda bahaushe kan ce, noma tushen arziki. Wannan ita ce mafita mai dorewa da za ta taimakawa nahiyar ba tare da ta tsaya jiran tsammani ba, domin wadancan manyan kasashe ba za su kawo mata daukin da ake fata ba.

Hakika kasar Sin na da gogewa a wannan fanni kasancewar bata da isasshen kasar noma, amma ita ke ciyar da al’ummarta har ma ta tallafawa wasu kasashen. Sin ta kasance aminiya ta kwarai mai kokarin lalubo hanyoyi masu dorewa na samun mafita ga kasashe masu tasowa, ba wai yin alkawari na fatar baki ba kadai ba. Kuma na san tabbas al’ummar Afrika sun san cewa kasar Sin da kamfanoni da masananta da ma jama’arta, su ne abokan hadin gwiwa na kwarai ba masu ci da guminsu ba.