logo

HAUSA

Bashir Ahmad: Ci gaban China ya ba ni mamaki sosai

2023-06-27 14:59:18 CMG Hausa

Kwanan nan, mai taimakawa tsohon shugaban tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari kan sababbin kafafen yada labarai, malam Bashir Ahmad, ya kawo ziyarar aiki kasar Sin tare da yin karatu a jami’ar Peking, daya daga cikin fitattun jami’o’in kasar.

Murtala Zhang ya samu damar zantawa da shi, inda ya waiwayi yanayin karatu da rayuwa da ya yi a kasar Sin a wannan karo, da yadda ya yi mu’amala da mutanen Sin, gami da yadda yake kallon ci gaban kasar. Malam Bashir ya kuma bayyana fatan sa ga ci gaban dangantakar kasar Sin da kasashen Afirka. (Murtala Zhang)