logo

HAUSA

Messi ya yi matukar jan hankalin Sinawa masu sha’awar kwallon kafa

2023-06-26 10:41:04 CMG Hausa

Ko shakka ba bu zuwan tauraron dan wasan kwallon kafar nan dan asalin kasar Agentina Lionel Messi kasar Sin ta ja hankali, inda tururuwar masu zuwa domin yin tozali da shi suka cike hanyoyin tafiyar kasa, dake wasu sassan birnin Beijing. Duk da tsananin zafi da ake fuskanta yanzu haka a babban birnin kasar ta Sin, wanda mizanin sa ya kai degrees Celsius 38 a ranar Alhamis, hakan bai hana matashiya Lin Xue zuwa kallon tauraron dan wasan kwallon kafar ba. Lin wadda ke karatu a jami’a, ta zo birnin Beijing tun daga birnin Shenzhen dake bakin teku, tana kuma cikin dumbin matasa masoya da suka ganewa idanun su zuwan Lionel Messi birnin Beijing.

Matashiyar dai ta yi jiran sama da sa’o’i 3 a filin wasa na ‘Workers' Stadium” dake birnin Beijing, kafin fara buga wasan sada zumunta da aka fafata tsakanin Argentina da Australia. Da take tsokaci kan hakan, Lin ta ce "Ba a zabar ranar kallon wasa", ta fadi hakan yayin da take shafa man kare fata daga zafin rana. Ta ce "wannan wata dama ce da ba kasafai ake samun irin ta ba, don haka ba zai yiwu na bari ta wuce ni ba, komin ruwa ko zafin rana".

Lin na da dalilai masu yawa da suka sa ta zuwa kallon wannan wasa, ciki har da kiyaye wannan muhimmin lokaci na tarihi. Wannan ne dai karon farko da Messi ya buga wasa a waje, tun bayan daga kofin duniya a kasar Qatar a watan Disambar bara, kana shi ne karon farko da Messi ya fita wata kasar waje don buga wasa, tun bayan da tauraro na Balon d'Or karo 7, ya ayyana cewa zai koma taka leda a yankin South Beach na birnin Miami na Amurka, a wata sauyin sheka mai ban mamaki.

Da yake tsokaci kan ziyarar ta Messi, shi ma wani magoyin bayan sa mai suna Sun, cewa ya yi "Wa zai bar wannan dama ta wuce shi, ta ganin tauraron dan wasan kwallon kafar duniya?" Sun wanda ke sanye da kayan kwallon kasar Argentina ya kara da cewa "Messi ba ya bukatar lashe kofin duniya kafin ya tabbatar wa duniya shi ne na daya, amma lashe kofin da ya yi ya burge ni, kasancewar sa kofi daya tilo da Messi bai taba lashewa ba a tarihin kwallon kafar sa. Ina takaicin kasancewar a yanzu Messi ya kai shekaru 35 a duniya, don haka zai yi wuya na sake samun damar ganin haskawar sa a nan gaba."

Magoya baya irin su Lin da Sun, za su iya ba da komai domin su ga tauraron da suke bege a rayuwar su, amma fa sai da suka kai ruwa rana kafin su dace da cimma burin na wannan karo. Domin kuwa tikitin wasan na ranar Alhamis din makon jiya da bai wuce kudin Sin yuan 580, wato kimamin dalar Amurka 80 ba, farashin sa ya tashi har zuwa yuan 4,800 kwatankwacin dala 662.

Game da hakan, Sun ya ce "Idan an kwatanta da rububin samun tikitin shiga kallon wannan wasa, zafin ranar da nake ji ba komai ba ne", ya fadi hakan yana share gumi daga goshin sa. Ya ce "Ban zata tikitin wasannan zai yi wahala haka ba, la’akari da tsadar da tikitin ya yi, gaskiya ban zata masoya kwallon kafa za su nuna karsashin su kamar wannan wasa ba. Manhajar sayar da tikitin ta rika samun matsala sau da dama. Sai mutum ya yi sa’a matuka kafin ya yi nasarar samun tikitin wasan nan."

A cikin filin wasan kuwa, masu kallo sun taru matuka. Zai yi wuya mutum ya ga irin wannan taron a filin wasa. Ko ina ka duba sai riguna da kayan wasa na kwaikwayon wadanda Messi ke sakawa kake gani, inda masu sayar da irin wadannan kayan wasa suka rika sayarwa baki daya.

Yayin wani tsokaci da ya yi gabanin take wasan, cikin raha, kocin Australia Graham Arnold ya ce "Zan so a ce an baiwa Messi wani kaso na kudaden rigunan Argentina da aka sayar kafin wannan wasa. Ban taba ganin rigunan Argentina dauke da lamba 10 masu yawan na wannan karon ba!"

A daya bangaren kuma, ana iya ganin kyamarori ta ko ina, yayin da ‘yan jarida da masu daukar hotuna, da masu shirya kananan fina finai ke ta gaggawar daukar bayanai da hotuna game da Messi.

Kafin take wasa, ‘yan kallo sun rika shewa lokacin da aka kira sunan Messi a jerin ‘yan wasa masu taka leda. Kaza lika an rika shewa yayin da alkalin wasa Ma Ning, ya busa usir din take wasa.

Daga take wasan kuma, cikin dakika 80, Mathew Leckie ya yi kuskuren sakin kwallo, wanda hakan ya baiwa Enzo Fernandez damar mikawa Messi kwallon, wanda kuma nan da nan ya yanke ‘yan bayan Australia biyu kafin ya jefa kwallo a raga.

A cewar kafar watsa bayanan wasanni ta “Gracenote”, da wannan tarihi, Messi ya samu nasarar cin kwallo a dukkanin mintunan wasa, in ban da minti na farko. Kaza lika kwallon da ya ci a wannan wasa ita ce mafi sauri da ya ci a tarihin taka ledar sa.

Bayan wasan, Messi ya ce "Na ji dadin kasancewa da kungiyar kasa ta. Kuma ina godewa daukacin masoyan kwallon kafa a kasar Sin bisa goyon bayan da suke ci gaba da nuna mana."

Ana iya cewa, duk da Messi na kara tunkarar karshen sana’ar sa ta kwallon kafa, har yanzu tauraruwar sa bata daina haskawa ba, duba da yadda yake kara burge masoyan sa. Har yanzu bai rasa kwarewar sa ta sarrafa kwallo, da rike ta da nuna gwaninta da ita ba. Yayin wasan da ya gabata, sama da ‘yan kallo 50,000 sun rika shewa suna jinjinawa Messi, yayin da wasan ke gudana, kuma har karshen wasan magoya bayan sa ba su daina jinjina masa ba.

Sai dai kuma a nata bangare, Australia ta dage wajen kaddamar da hare hare kan kungiyar Argentina, ta yadda ita ma ta taka rawar gani sosai a yayin wasan. Amma duk da haka, Messi ya jagoranci Argentina ta yadda ta kai ga samun nasarar wasan. A minti na 68 dan wasan Argentina  German Pezzella ya jefa kwallo ta 2 a ragar Australia.

Kafin wannan lokaci, shekaru 5 da suka gabata Messi ya ziyarci kasar Sin, a kuma wannan lokaci ma ya zo a gabar da masoyan sa suka yi masa babbar tarba mai ban sha’awa. A tsakiyar wasan da aka buga, wani magoyin bayan Messi sanye da riga irin ta sa, ya ruga a guje cikin filin wasan, inda ya rika kaucewa masu tsaron filin, har ya kai ga zuwa inda Messi yake ya rungume shi.

Duk da cewa karya ka’ida ne dan kallo ya shiga fili yayin da ake wasa, a daya hannun wannan matashi ya zama abun kishi tsakanin miliyoyin masu goyon bayan Messi, dake sassa daban daban na duniya, bisa damar da ya samu ta gaisawa kai tsaye tare da tauraron na sa. Wannan tasiri ne na martabar Messi, dan wasan da ya kafa tarihi mai ban sha’awa a fannin kwallon kafa. Ana iya cewa, kaunar da ake nuna masa ita ce babbar martaba da Messi ya samu baya ga kwallon kafa. Messi ya zamo dan wasa da ya samu goyon baya, da kauna da masoyansa za su jima suna rike da ita a zukatan su.