Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya
2023-06-26 15:50:59 CMG HAUSA
DAGA YAHAYA
Shin ƙasar Sin da Turai za su iya ƙare tsarin ƙasa da ƙasa a bayyane?
Yayin da al'ummomin kasa da kasa ke fama da ƙaruwar rashin tabbas daga rikice-rikicen siyasa, da ci gaban juna, ra'ayin da a da ake ɗaukarsa a matsayin ci gaba na 'yantar da ƙasa da ƙasa da dunkulewar duniya, yanzu yana fuskantar babban ƙalubale. Ƙasar Amurka, a da ta kasance shugabar duniya, amma yanzu ta tsinci kanta cikin kacaniyar siyasar duniya. Kama daga tsoma baki a harkar ƙasar Sin zuwa adawa da kasar Rasha da katsalandan a Gabas ta Tsakiya, Amurka tana daɗa kunyanta kanta game da abin da take kira “kishin ƙasarta” a maimakon nazarin matsaloli ta mahangar duniya.
Duk da sanin cewa rikice-rikicen da ƙasashen duniya ke ciki ya haifar da cikas ga kasuwannin duniya wanda ya haifar da koma baya a fannin tattalin arziki da yunwa, har yanzu Amurka ba ta damu da buƙatun duniya ba, musamman ƙasashe masu tasowa, ta zaɓi ta bi hanyar da ba za ta bulla ba. Lokacin da Amurka ta ga alaƙar Latin Amurka da ƙasar Sin ta bunƙasa cikin sauri, sai da ɗauki wannan alaƙar a matsayin barazana maimakon damar da za ta sanya wasu kwanciyar hankali da wadatar ƙasashen da take ɗauka a matsayin "maƙwabtarta." A lokacin da Amurka ta ga kamfanonin Turai na ƙoƙarin tabbatar da ra’ayinsu ta hanyar zuba jari a ƙasar Sin, Amurka na kallon hakan a matsayin wata barazana da ya kamata a yi taƙa-tsantsan. Fadada tasirin ƙasar Sin zuwa ga sauran ƙasashen duniya, duk da ƙasashen duniya sun tabbatar da tasirin na taimakawa ga zaman lafiyar duniya, Amurka na kallon wannan tasiri a matsayin ƙalubale da hadari.
A cikin jawaban firaministan kasar Sin yayin ziyararsa a Turai a baya-bayan nan ya ce, ƙasar Sin na ɗauke da wani ra'ayi na daban. Inda ya buƙaci hukumar ba da lamuni ta duniya IMF, da bankin duniya da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa su kammala wani sabon zagaye na yin gyare-gyare kan yawan ƙuri'u da hakkin zaɓe, da ƙara yawan muryoyin kasuwanni masu tasowa da ƙasashe masu tasowa. Ya kuma buƙaci ƙasashen da suka ci gaba da su cika alkawuran da suka ɗauka na bayar da taimako da tallafin kuɗi ga ƙasashe masu tasowa.
A yayin jawabinsa, Li ya jaddada cewa, ƙasar Sin, tare da ƙasashen duniya, sun sa ƙaimi ga samar da 'yancin yin ciniki da zuba jari, da samar da sauki, kuma suna adawa da son kai, da wargajewa, da dakile hanyoyin samar da kayayyaki ta kowace fuska. Yayin da tsarin bai daya da son kai ke yaduwa, dole ne wani ya tsaya tsayin daka kan hadin gwiwar ƙasa da ƙasa da neman ci gaban juna.
Ƙasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da inganta wannan tsari ga duniya. Turai a nata ɓangaren kuma, ko da yake tana fuskantar matsin lamba daga ketaren Atlantika, tana kuma neman hanyar cimma manufofin waje mai cin gashin kanta. A matsayinsu na ƙasashe biyu waɗanda tattalin arzikinsu na daga cikin manyan tattalin arziki a duniya wato ƙasar Sin da Turai, hakkin nemo hanyar ci gaban duniya ya rataya a wuyarsu.
To a daidai wannan gaɓa, sai mu ce "Dabara ta rage ga mai shiga rijiya” . (Yahaya)