logo

HAUSA

Sin da Turai ba za su katse hulda ba

2023-06-25 19:50:47 CMG HAUSA

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya kammala ziyararsa a Jamus, da Faransa, ya kuma dawo nan birnin Beijing a jiya Asabar. A cikin mako da ya gabata, ya zanta da wakilan kasashen biyu a fannin siyasa, da masana’antu, da kasuwanci, inda ya jadadda cewa, bunkasuwar kasar Sin ta kawowa dukkanin fadin duniya damammaki maimakon hadari.

A nasu bangaren, shugabannin kasashen biyu sun bayyana matsayin da suke kai na kin yarda, ko rashin amincewa da ra’ayin katse huldar bangarorin biyu, da ma yaki da ko wane irin mataki na jayayya da juna. Sun kuma bayyana cewa, Sin da Turai na da matsaya daya game da kin katse huldarsu, da ingiza hadin kai, da samarwa duniya tabbaci bisa hali mai sarkakiya da duniya ke ciki.

Tun daga karshen bara, shugabannin Sin da Turai na kara yaukaka mu’ammala, da tuntubar juna. Kuma shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da dai sauran shugabannin kasashen Turai, sun ziyarci kasar Sin, tare da cimma matsaya daya bi da bi da shugaban Sin, kan yadda za su zurfafa dangantaka da hadin kansu.

A daya bangaren kuma, ziyarar Li Qiang ta wannan karo a Turai, na da zummar tabbatar da matsaya daya da aka cimma, da ingiza hadin kansu a fannoni daban-daban. (Amina Xu)