logo

HAUSA

Bikin gargajiya na Sinawa da ake kira Duanwu

2023-06-23 17:55:25 CRI

Bikin Duanwu na daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na kasar Sin, wanda ke da dogon tarihi, domin kuwa bisa tarihi an kai shekaru kimanin dubu biyu ana gudanar da shi, kuma a kan yi wannan biki ne a ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma kamar yadda ka fada, a wannan shekara, ya fado daidai a jiya Alhamis, wato 22 ga watan Yuni. Ana kuma kiran bikin da sunaye iri iri, misali, bikin Duanyang, bikin watan Mayu, bikin mawaka, bikin tseren kwale-kwale da sauransu.

Game da asalin bikin, a bayanan da masana tarihi suka rubuta, an ce, bikin ya samo asali ne daga al’adun kabilar Wuyue da ke kudancin kasar Sin, wadanda a lokacinsu, bikin ya kasance biki na ibada. Amma yanzu, an fi danganta bikin ne ga shahararen marubucin wake-waken nan mai suna Qu Yuan, wanda ya burge al’ummar kasar Sin sosai da yadda yake matukar kishin kasarsa, da kuma wake-waken da ya rubuta.(Lubabatu)