logo

HAUSA

Karuwar nuna wariya alama ce ta koma bayan kare hakkin bil Adama

2023-06-22 17:58:01 CMG Hausa

Batun kare hakkin bil adama tsakanin manyan kasashe masu karfin fada aji, na cikin muhimman batutuwa dake jan hankali masharhanta a sassan duniya daban daban.

Ko shakka ba bu, ba wata al’umma da ba ta fatan samun cikakkiyar kariya a fannonin hakkin bil adama daban daban, musamman a wannan lokaci da duniya ke samun ci gaba, da dunkulewa, ake kuma burin ganin dan adam ya yi rayuwa mai yalwa da walwala.

To sai dai kuma wani abun lura a nan shi ne, yadda al’ummu daban daban ke kallon ma’anar kare hakkin bil adama, inda yayin da wasu ke kallon batun a matsayin wata manufa samar da ci gaba, da walwala, da gina al’ummar dan adam mai kyakkyawar makoma, wasu kuwa na amfani da batun kare hakkin bil adama ne a matsayin hanyar cin gajiyar siyasa, da nuna cewa su ne mafiya kwarewa a wannan fage.

Ga misali, a nan kasar Sin, akidar kare hakkin bil adama na nufin kare rayuka da walwalar al’umma, da wanzar da zaman lafiya da ci gaban zamantakewar daukacin al’ummar kasa, da zamanantar da kasa daga dukkanin fannoni. Kuma Sin ta amince cewa ba wata hanya dala tilo da za a ce ita ce kadai wadda bil adama zai bi wajen tabbatar da kare hakkokin bil adama, illa dai kawai ko wace kasa, ko yanki ya yi amfani da yanayin da yake ciki, wajen cimma nasarar kare hakkin al’ummar sa.

A daya bangaren kuwa, kasashen yamma, musamman Amurka, na kallon kan ta a matsayin mafi kwarewa, wadda kuma ta cancanci ta koyar da duniya yadda ake kare hakkokin dan adam, har ma a wasu lokutan ‘yan siyasar ta ke nuna yatsa ga sauran sassa, kan yadda suke aiwatar da na su manufofin na kare hakkin bil adama. To amma Bahaushe kan ce “Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo”, wato dai ko wace kasa, ita ta fi sanin yanayi mafi dacewa na matakan da za ta iya aiwatarwa domin kare al’ummar ta daga fadawa rikici, ko gurguncewar hakkin al’ummar ta.

Kaza lika, a yayin da Amurka ke sukar sauran sassa da gazawa wajen kare hakkokin al’umma, kamata ya yi ta fara duba matsalolin ta na cikin gida, kamar batun nuna wariyar launin fata da ya zama ruwan dare a kasar.

Masharhanta na cewa, alamar ci gaban al’umma na bayyana ne daga imanin al’umma da makomar su.

Wani sharhi da jaridar “Washington Post” ta wallafa a baya bayan, ya nuna sakamakon wani bincike da aka gudanar game da wariyar launin fata a Amurka, wanda ya tabbatar da cewa, kaso mafi rinjaye na Amurkawa masu asali daga Afirka sun damu, da yadda ake samun karuwar nuna wariyar launin fata gare su a shekarun baya bayan nan, sama da yadda abun yake a baya.

Kaza lika, sakamakon binciken ya nuna rashin gamsuwa da wannan rukuni na al’ummar Amurka ke da shi don gane da kyautatuwar yanayin kare hakkokin su, ciki har da na zamantakewa, da rashin daidaito a fannin tattalin arziki, da kula da lafiya, da batun fuskantar hare haren bindiga da dai sauran su.

Idan mun yi la’akari da sakamakon wannan bincike, za mu iya gano cewa, Amurka na da na ta manyan matsaloli na kare hakkin dan adam, wadanda ya kamata ta tunkara, maimakon mayar da hankali ga sukar yadda wasu kasashen na daban ke kokari karewa al’ummun su hakkoki. Idan kuwa Amurka ba ta dauki wannan mataki ba, to sakamakon da za ta ci gaba da samu a cikin gida, zai dada tabbatar da kallon da wasu masu fashin baki ke mata, na mai take laifin ta domin hangen na wasu. (Saminu)