Ba za’a bar kowace kasa a baya ba a tafarkin samar da ci gaba
2023-06-22 16:11:43 CMG Hausa
Samar da ci gaba, babbar mafita ce ga warware dukkanin matsaloli. A halin yanzu duniya na kara fuskantar matsaloli da dama, ciki har da rashin zaman lafiya, da yawaitar rikice-rikicen siyasa, da koma-bayan tattalin arziki. To, ina mafita? A ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2021, a yayin muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar samar da ci gaban dukkan duniya, inda aka maida hankali kan wasu muhimman fannonin hadin-gwiwa 8, wadda ta samu goyon-baya daga kasashe sama da 100 gami da kungiyoyin kasa da kasa da dama.
A ranar 24 ga watan Yunin shekara ta 2022, shugaba Xi ya jagoranci shawarwari tsakanin manyan jami’an kasashe daban-daban kan ci gaban duniya, inda ya bullo da wasu muhimman matakan hadin-gwiwa 32, da zummar aiwatar da shawarar samar da ci gaban duniya baki daya a zahirance.
Kawo yanzu, an riga an kammala rabin matakan, ko kuma samun nasarori. A fannin rage talauci, a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta taimaki kasashe masu tasowa kawar da talauci cikin sahihanci, ta hanyar kafa tsarin hadin-gwiwa, da yin mu’amalar matakan rage talauci, da gina wasu muhimman ayyukan more rayuwar al’umma da sauransu.
Babban dalilin da ya sa shawarar samar da ci gaban fadin duniya ta samu karbuwa sosai, shi ne domin ta tattara ra’ayoyin al’umma game da samar da ci gaba. Haka kuma, shawarar tana dora muhimmanci kan muradun jama’a, da taka rawa a wasu manyan fannonin hadin-gwiwa 8, wadanda suka shafi burikan samar da ci gaba mai dorewa guda 17, dake cikin ajandar samun ci gaba da MDD ta tsara nan da shekara ta 2030.
Kasar Sin tana bakin kokarin ta domin samar da ci gaba ga duk duniya, saboda a ganinta, ba za’a bar kowane mutum ko wata kasa a baya ba a tafarkin samar da ci gaba. (Murtala Zhang)