logo

HAUSA

Ba A Yabon Dan Kuturu…

2023-06-21 17:48:16 CMG Hausa

Daga ranar 18 zuwa 19 ga wannan wata ne, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kawo ziyara kasar Sin, ziyarar da masana suka ce tana da babbar ma’ana duk da cewa, yanzu dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala mafi tsanani, tun bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu, wanda bai dace da moriyar jama’ar kasashen biyu da ma begen da kasa da kasa ke yi ba.

Sin dai tana kokarin raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka cikin lumana da yadda hakan zai amfanawa duniya baki daya. Kana tana fatan kasar Amurka za ta fahimce ta bisa hakikanin yanayi, da yin kokari tare da kasar Sin din, wajen tabbatar da tushen siyasa na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da daidaita matsaloli yadda ya kamata, da kokarin aiwatar da shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a tsibirin Bali, da sa kaimi ga maido da dangantakarsu bisa turbar da ta dace.

Bangaren Amurka dai ya sha alkawarin mutunta alkaruwan da sassan biyu suka cimma a lokuta da matakai daban-daban don inganta alakar sassan biyu, amma sai a wayi gari Amurka ta sake mayar da hannun agogo baya.

A jawabinsa yayin ganawa da shugabannin Sin yayin ziyararsa a Beijing, Blinken ya bayyana cewa, Amurka na mutunta alkawuran da shugabannin kasashen suka ya yi, kuma Amurka ba ta neman "sabon yakin cacar baka", ba ta neman sauya tsarin kasar Sin, ba ta neman adawa da kasar Sin ta hanyar karfafa kawance, kana ba ta goyon bayan 'yancin kai na yankin Taiwan". Amurka ba ta da niyyar yin rikici da kasar Sin, kuma tana fatan yin mu'amala mai zurfi tsakanin manyan jami’anta da kasar Sin, da kiyaye hanyoyin tattaunawa marasa shinge, da warware bambance-bambancen dake tsakaninsu, da neman tattaunawa, da yin musaya da hadin gwiwa. Sai dai masu iya magana na cewa, ba a yabon dan kuturu sai ya shekara da yatsa. Ma’ana sai mun ga Amurka ta cika wadannan kalamai da ta fada.

Hanya mafi dacewa ta warware batutuwa da suka shafi kasa da kasa, ita ce tattaunawa, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da yin komai a bayyane, da damawa da kowa da kowa, tare da ci gaba da shawarwari da yin hadin gwiwa, maimakon yin fito na fito.

Haka kuma, ya dace a rika martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa, maimakon fakewa da wani batu na siyasa ko wata manufa da nufin cimma wata moriya ko neman tayar da fitina a sauran kasashe.

Sanin kowa ne cewa, takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki, kuma hakan ba zai taba iya magance matsalolin Amurka ko kuma kalubalen da duniya ke fuskanta ba. Sannan bai dace wani bangare ya yi kokarin siffanta daya bangaren bisa son ransa, sannan ya hana daya bangaren hakkinsa na samun ci gaba ba. Abin jira a gani dai shi ne, ko Amurka za ta cika alkawuranta? Kyawun alkawari dai aka ce cikawa. (Ibrahim Yaya)