logo

HAUSA

Takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki

2023-06-21 09:58:28 CMG Hausa

A wannan makon ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu manyan jami’an kasar da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang da Mr. Wang Yi, direktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, suka gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken wanda ya kawo wata ziyarar aiki kasar Sin.

Yayin ganawar, Xi ya yi nuni da cewa, duniya na bukatar kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, kana hanyar daidaita alakar kasashen biyu, na iya shafar makomar daukacin bil-Adama.

Haka kuma, takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki, kuma hakan ba zai taba iya magance matsalolin da Amurka ke fuskanta ko kuma kalubalen da duniya ke fuskanta ba. Bai dace wani bangare ya yi kokarin siffanta daya bangaren bisa son ransa, kuma har yanzu ya hana daya bangaren hakkinsa na samun ci gaba ba.

A ko da yaushe kasar Sin na fatan ganin alakar Sin da Amurka mai dorewa, kuma manyan kasashen biyu za su iya shawo kan matsaloli daban-daban, da lalubo hanyar da ta dace ta yin sulhu bisa mutunta juna, da zaman lafiya da hadin gwiwa tare da samun moriyar juna. Yana mai kira ga bangaren Amurka da ya rungumi dabi'ar nuna sanin ya kamata, da yin aiki tare da kasar Sin a cikin harkokin kasa da kasa.

A nasa bayanin, Blinken ya ce, Amurka na mutunta alkawuran da shugaba Biden ya yi, kana ba ta neman "sabon yakin cacar baka", ba ta neman sauya tsarin kasar Sin, ba ta neman adawa da kasar Sin ta hanyar karfafa kawance, kana ba ta goyon bayan "'yancin kai na yankin Taiwan". Amurka ba ta da niyyar yin rikici da kasar Sin, kuma tana fatan yin mu'amala mai zurfi tsakanin manyan jami’an ta da kasar Sin, da kiyaye hanyoyin tattaunawa marasa shinge, da warware bambance-bambancen dake tsakaninsu, da neman tattaunawa, da yin musaya da hadin gwiwa. Ya kamata manyan kasashe su fahimci cewa, yin fito na fito bai dace da moriyar kasashen duniya ba. (Saminu, Ibrahim. Sanusi Chen)