logo

HAUSA

An cika shekaru 20 da fara zirga-zirgar jiragen ruwa ta birkin jiragen ruwa na madatsar ruwa ta Sanxia

2023-06-21 10:12:50 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barkanmu da war haka! Kamar yadda muka sani, a bana ne, ake cika shekaru 20 da fara zirga-zirgar jiragen ruwan al’umma, ta birkin jiragen ruwa da ke madatsar ruwan “Three Gorges” ko kuma Sanxia a Sinance. Cikin wadannan shekaru 20, an yi amfani da birkin har sama da sau dubu 193, yayin da jiragen ruwa sama da dubu 993, da fasinjoji kimanin miliyan 12 da dubu 239 suka wuce ta birkin. Kuma yawan hajojin da aka yi jigilar su ta birkin ya kai tan biliyan 1 da miliyan 910.