logo

HAUSA

Beijing, fitaccen birni ne wajen kare nau’ikan halittu mabambanta

2023-06-20 16:08:39 CMG HAUSA

 Birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin yana kara azama matuka a fannin kare muhallin halittu a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kuma tuni ya samu babban sakamako, inda ya kasance daya daga cikin manyan birane wadanda suka fi rinjaye, a bangaren kare nau’o’in halittu mabambanta a fadin duniya:

Beijing, muhimmin wuri ne da tsuntsaye suke wucewa yayin kaura bisa sauyawar yanayi, inda ake iya ganin tsuntsaye da yawan gaske suke hutu ko wucewa a cikin shekara, musamman ma a cikin ‘yan shekarun baya bayan nan, a kan ga wasu tsuntsaye masu daraja a Beijing, sakamakon kyautatuwar muhallin birnin. Kawo yanzu nau’ikan tsuntsaye dake rayuwa a birnin sun kai 515.

Wani abun faranta rai ma shi ne, nau’ikan halittun birnin sun kai 3,560 a shekarar bara ta 2022, kuma yankin daji a birnin ya kai kaso 44.8 bisa dari a karshen bara.

Haka zalika, an gina sabbin lambunan shan iska 180 a Beijing a cikin shekaru biyar da suka gabata, inda mazauna birnin suke iya motsa jiki a kusa da gidajensu.