logo

HAUSA

Amurka Wadda Ke Tayar Da Yake-Yake A Duniya Ta Haifar Da Rikicin ’Yan Gudun Hijira

2023-06-20 15:12:12 CMG HAUSA

DAGA MINA

Yau, ranar ’yan gudun hijira ce ta kasa da kasa. Na zana wani yaro mai suna Alan Kurdi, mai shekaru 3 kacal a duniya, ya mutu kan hanyarsa ta gudun hijira, bayan da ya rasa gidansu sanadiyyar yaki a kasar Sham.

Amma, bakin ciki shi ne, a kullum ana samun yara irinsu Alan Kurdi dake rasa rayukansu saboda yake-yake. Alkaluman kididdiga da hukumar kula da kaurar jama’a ta kasa da kasa ta fitar na nuna cewa, tun daga shekarar 2014, yawan ’yan kasar Sham dake gudun hijira, kuma suka mutu a kan hanyarsu ta neman tsira ya haura dubu 29. Baya ga miliyan 5.4 dake gudun hijira a wasu kasashe, yayin da wasu miliyan 13.5 kuma ke matukar bukatar tallafin jin kai.

A halin yanzu, kashi 72% na ’yan gudun hijira a duniya, sun fito ne daga kasashen Sham da Venezuela da Ukraine da Afghanistan da Sudan ta kudu. Rikicin ’yan gudun hijira da wadannan kasashe suke fuskanta na da alaka sosai da Amurka, saboda tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen da kuma amfani da karfin tuwo da gwamnatin Amurka take yi. MDD ta ba da alkaluma cewa, tun barkewar yakin Sham a shekarar 2011, matakan soja da Amurka ta dauka a Sham, sun haifar da mutuwar mutane a kalla dubu 350, yayin da rabin al’ummar kasar ke gudun hijira, ga matsalar gidaje da ta abinci, abin da ya zama rikicin jin kai mafi tsananni tun lokacin da aka kawo karshen yakin duniya na biyu.

An dauki hoton Alan Kurdi wanda ya mutu a gabar teku a shekarar 2015, abin da ya girgiza duk duniya baki daya, tare da sosan ran mutane. Amma ’yan siyasa na Amurka sun nuna halin ko-in-kula, suna ci gaba da daukar matakin soja a duniya. Amurka mai haifar da rikicin ’yan gudun hijira, ba ta kula da hakkin bil Adama, sai moriyar siyasa kawai. Muna fatan a dakatar da yake-yake a duniya, don ceton rayukan kananan yara kamar Alan Kurdi. Amma wannan fata ba zai taba tabbata a duniya ba, sai ’yan siyasar Amurka sun yi watsi da moriyar kashin kai, sun yi la’akari da hakkin bil Adama, musamman ma hakkin kare rayukan kananan yara a duniya. (Mai zana da rubuta: MINA)